Illolin Luwadi Da Hukuncinsa

0 267

Luwadi da Madigo sun zama ruwan dare a tsakanin matasa maza da mata a wannan zamani. Sun biye wa sha’awa irin ta shaidanci, sun afka cikin mafi kazantar laifin da aka taba aikatawa a bayan kasa.

Hakika duk cikin nau’o’in Zina da danginta, Luwadi shi ne mafi muni, kuma mafi kazanta. Kamar yadda Allah (S.W.T) ya ke cewa a cikin Alkur’ani Mai girma: “KA TUNA ANNABI LUD, LOKACIN DA YA CE WA MUTANENSA”, “ME YA SA KU KE AIKATA IRIN WANNAN ALFASHA (ALFASHAR DA BABU WANI WANDA YA RIGA KU AIKATAWA DAGA CIKIN TALIKAI, WATO HALITTU BAKI DAYA)?”. “KU KUNA ZO WA MAZAJE TA BANGAREN SHA’AWARKU MAIMAKON MATAYE, BARI DAI, KU MUTANE NE MA SU MATUKAR BARNA”. (Suratul A’araf, aya ta 80, zuwa 81).

Kuma sabo da munin laifinsu, shi ya sa Allah ya yi ma su azabar da bai taba yi wa kowa kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala’iku su ka ciccibi garin zuwa sama, suka watsa narkon Azaba, sannan su ka kifar da su.

A cikin Suratul Hud, Allah (S.W.T) ya ce: “YAYIN DA AL’AMARINMU YA ZO, SAI MU KA SANYA SAMAN BIRNIN YA ZAMA KASANTA (WATO MU KA KIFAR DA BIRNIN), SANNAN MU KA YI MA SU RUWAN DUWATSUN WUTA NA
SIJJEEL”. Kamar yadda Allah (S.W.T) ya ke cewa: “SAI MU KA YI RUWAN (DUWATSUN AZABA) A KANSU, LALLAI RUWAN DUWATSUN AZABAR NAN TA WADANDA AKA YI MA SU GARGADI YA YI MUNI KWARAI”. (Suratun Namli, aya ta 58).

Sabo da tsananin bala’in da ke cikin wannan aika-aikar, Manzon Allah (S.A.W) ya ke cewa: “MAFI GIRMAN ABIN DA NA KE TSORACE WA AL’UMMATA, SHI NE; IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD (A.S)”. (Tirmizy ya ruwaito shi a cikin Sunan, Hadisi na 1,457, Ibnu Majah, Hadisi na 2,563).
.
A cikin wani hadisin Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “TSINANNE NE, DUK WANDA YA YI JIMA’I DA DABBA,
KUMA TSINANNE NE, DUK WANDA YA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD (A.S)”. (Imam Ahmad ne ya ruwaito shi a cikin Musnad, Hadisi na 1,878).

A cikin wani hadisin kuma, Manzon Allah (S.A.W) ya fadi irin hukuncin da shari’ar Musulunci ta tanadarwa ma su Luwadi, inda ya ke cewa: “DUK WANDA KU KA KAMA YA NA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD, TO, KU KASHE MAI AIKATAWAR DA KUMA WANDA AKE AIKATA MA SA”. (Sunanut Tirmizy, Hadisi na 1,456, da Sunanu Abu Dawud, Hadisi na 4,462, da kuma Sunanu Ibnu Majah, Hadisi na 2,561).

Luwadi da Madigo mummunar Annoba ce wadda ta kaucewa hanyar da Allah ya halicci dukkan halittunsa akai, don ko dabbobi ba za ka samu su na yin irin wannan ba.

Shi ya sa Annabi Lud (A.S) ya ce wa mutanensa: “KUN ZO DA ALFASHA WADDA BABU WANI DAGA CIKIN HALITTU (MUTANE KO ALJANU KO DABBOBI) WANDA YA RIGA KU AIKATAWA”.

Imam Ibnul Qayyim Aljawziyyah ya ce: “Dukkansu guda biyun (Zina da Luwadi ko Madigo), su na kunshe da mummunar alfashar da ta kaucewa Fitrar Allah. Kuma Luwadi ya na kunshe da bala’o’in da ba za su kidayu ba. Kuma duk wanda aka yi Luwadi da shi, zai gwammaci gara ya mutu da ace an aikata wannan fasadi da shi,
domin idan ya riga aka yi da shi, to, zuciyarsa za ta riga ta yi lalacewar da babu sauran tsammanin daidaituwarsa ko kuma dawowarsa akan hanya, kuma ba zai sake jin wata sauran kunya ko a wajen Allah (S.W.T) da halittunsa ba. Kuma ruwan MANIYYIN da mai Luwadin ya zuba, ya na zama a cikin wanda aka zubawa, baya narkewa har ya zama tsutsotsi sabo da ba shi da Mahaifa, duk lokacin da tsutsotsin su ka bukaci Abinci, in babu wannan Maniyyi, sai su rika cin naman jikin Dan adam, ya zama kamar guba ne a jikinsa da kuma ruhinsa (shi ya sa ya na da wuya su iya yin cikakkiyar tuba wadda Allah ya ke so). Kuma duk lokacin da abun ya motsa ma su, sai sun je sun yi, ko kuma anyi da su.

Ibnul Qayyim Aljawziyyah ya ci gaba da cewa: “Malamai sun yi sabani akan cewa: “SHIN ‘YAN LUWADI ZA SU SHIGA ALJANNAH, KO KUMA HAR ABADA BA ZA SU SHIGA BA?”. Na taba jin Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya na bayanin ra’ayin Malamai akan haka. (A duba Aljawabul Kafiy, shafi na 115).

Shi ya sa shari’ar Musulunci ta ce; kashewar ita ce mafi alheri a gare shi, fiye da rayuwa cikin kaskanci, da wulakanci, da kuma rashin Imani. Kira: Ya ku bayin Allah, ku tuba zuwa ga Allah, ku sani cewa; rahamar Allah ta na da yalwa, kuma ALLAH ya na son ma su tuba. KA CE MA SU: “YA KU BAYI NA WADANDA SU KA YI
WA KANSU BARNA, KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH, HAKIKA ALLAH YA NA GAFARTA DUKKAN ZUNUBAI BAKI DAYA, SHI SHI NE MAI GAFARA KUMA MAI JIN KAI”. (Suratuz Zumar, aya ta 53). Ku nisanci miyagun Abokai, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “MUTUM YA NA BIN ADDININ ABOKINSA NE, DON HAKA KOWANENKU YA KULA DA WANDA ZAI YI ABOTA DA SHI”. (Sunanut Tirmizy, Hadisi na 2,378).

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...