Tunatarwa: Ranar Alhamis Za A Yi Tsayuwar Arfa A Saudiyya

0 181

Gwamnatin Saudiyya ta bada rahoton kan ranar da za ayi tsayuwar Arfa inda ta ce ba’a ga jinjirin watan Dhul-Hijjah a ƙasar ranar Litinin ba kamar yadda ake tsamnanin sa a lissafin kalandar ƙasar, Saboda haka yau Talata zai zama 30 ga watan zul-qaada, Arafah kuma zai zama ranar Alhamis 31 ga watan Agusta, kana ranar Juma’a ita ce ranar Sallar laiya a kasar Saudiyya.

Haka zalika a Nijeriya yau Talata shine 29 ga watan Dhul-Qadah a lissafin ganin watan ƙasar, kuma yau ne Sarkin musulmin ƙasar, Muhammad Abubakar Sa’ad III ya bada shelar fara duba jinjirin wata a faɗin ƙasar, da fatan in an gani za’a sanar da mahukunta har ya kai ga Sarkin Musulmi.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...