GIDANA: Tarbiyya a gidan Musulmi da matakan samunta Kashi Na Daya- Hadiza Balanti

0 394

Dukkan godiya da yabo da kirari da Jalalah da daukaka sun tabbata Allah madaukakin sarki, sarki Allah mabuwayi mai iko da isa, sarkin da bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba, sannan babu wani abin halitta daya zama gini ko tamka a gareshi.

 

Tsira daraja da aminci, su kara tabbata ga Annabin Rahma Annabi Muhammad SAW tare da alayensa da dukkanin Sahabbansa da masu bin tsarin koyarwarsu sau da kafa cikin kyautatawa har izuwa ranar karshe.

 

‘Yan uwana masu albarka, ina karanta muku gaisuwa da addua tare da fatan alkhair mai yawa, Allah ya zama gatanmu gabadaya, amin.

 

In sha Allah, kamar yadda na alkawarta daga yau a duk mako idan Allah ya ara mana rai da lafiya da lokaci, zan dinga kawo muku rubutu akan TARBIYYA A GIDAN MUSULUNCI DA MATAKAN DA IDAN AKA BI ZAA DACE DA KYAKKYAWAR TARBIYYAR wanda na bashi suna kamar haka;

GIDANA
da fatan da zarar an ga kuskure ko zarmiya zaa gyara min ko a nusar dani kuskuren domin gyarawa in sha Allah.

 

Bismillahi Rahmanir Rahim.
Malaman Tarbiyya sun kasa nau’in (Tarbiyya) zuwa gida uku Wanda cikin yarda ta Allah zamuyi bayaninsu daki-daki.

 

1. Akwai tarbiyya (asas) ma’ana tarbiyar da yaro yake bukata  daga haihuwarsa  zuwa lokacin da zai fara rarrafe har ya fara magana da wasa da yara yan uwansa.

 

Wannan tarbiyya hakkin  iyaye ce (wato uwa da uba duka) domin itace matakin farko na samun tarbiyyar, musamman mahaifiya don itace kan gaba wajan bada wannan tarbiyya.

 

Ya kamata masu tarbiyya su lura su gane, idan aka rasa wannan tarbiyya zaiyi wuya a samu abinda akeso, kuma ta yiwu tun daga wannan lokaci zaayi ta kitso da kwarkwata, wal’iyazu Billah.

 

2. Akwai Tarbiyya ( mujtama’a) wato itace Tarbiyyar da yaro yake samu a waje wato cikin unguwarsu ko kuma garinsu ko yankinsu da dai sauransu.

 

Wannan tarbiyyar ta kan kasance ne gwargwadon wajen da yaro ya taso da kuma yanayin yaran da yake wasa dasu idan ya fita waje domin ana tasirantuwa da yanayin wajan da mutum ya taso idan ya taso a gari ko kuma unguwa mai tarbiyya.

 

3. Akwai Tarbiyya (madarisa)   itace wadda yaro zai samu a makaranta yayin daya fara karatu wannan tarbiyya tana hannun malamai, domin hakkinsu ne kula dashi da bashi tarbiyya a makaranta da kuma dora shi a hanyar data dace da kuma kokarin raba shi da dabi’a mara kyau.

 

Mu hadu a Gidana kashi na biyu.

 

A madadin cibiyar yada alkhair da inganta zamantakewa ta DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY da dukkanin ma’aikatanta da ma’abotanta da masoyanta, nake muku addu’a tare da fatan alkhair.
___________________________
Masu son kasancewa tare damu a sauran kafofinmu na sadarwa, suna iya bin wadannan matakai kamar haka;

WHATSAPP: +2348122228484

BLOG: http://www.dakeake.wordpress.com

FACEBOOK PAGE: www.facebook.com/dakeakeglobal/

TWITTER: https://twitter.com/dakeake

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/dakeake/

HASHTAG: #dakeake

Hadiza Balanti
CEO
DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...