Hoto: Taurarin Shirin Series Da Ke Samun Sama Da Dala $500,000 A Kowane Kashi

0 175

Wadannan ‘yan wasan kwaikwayo suna samun akalla sama dala $500,000 a kowane jigon series da suka fito a ciki, akalla za a iya cewa sune jiga-jigan ‘yan wasan kwaikwayo da aka fi biya kudi a duk fadin Duniya idan aka zo ta harkar da ya shafi series.

1. Taurarai wadanda aka fi biya su ne ‘yan wasan series na “The Big Bang Theory”, ana biyan su dala $900,000

 

2. Tsoho mai ran karfe Robert De Niro ya zo na biyu a sabuwar series din zai fito mai suna “The Wizard of Lies”, inda ake biyan sa dala $775,000.

 

3. Dwayne Johnson wanda aka fi sane da suna ‘”The Rock” sanda yake wasan danben kokawa ta wrestling, shi ya zo na biyu a wannan jerin. Dwayne na samun  dala $650,000 a shirin series na “Balllers”.

 

4. Babban dan wasan kwaikwayo na shirin series din “NCIS” Mark Harmon na samun dala $525,000 a kowane kashi da ya fito.

 

5. A wannan jerin Shahararrun taurarin ‘yan wasan kwaikwayon 13 suka fado a wannan jerin, series din sun hada da sanannen shirin series din “Game of Thrones” na samun dala $500,000.

 

– Dan wasan kwaikwayo na series din “House of Cards” of cards Kevin Spacey shi ma yana samun dala $500,000 a kowane … a series din.

– Kevin Costner na series din “Yellow Stone” shi ma yana sama dala $500,000 kamar yadda sauran ‘yan wasan kwaikwayo da ke jerin nan ke samu.

– Jaruman taurarin series din  “Modern Family” su ma ana biyan kowane daga dala $500,000.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...