Wayne Rooney Ya Yi Ritaya Daga Bugawa Ingila Tamaula

0 130

Tsohon kyaftin din kungiyar Manchester United da tawagar kwallon kafa ta Ingila, Wayne Rooney ya bayyana yin ritaya daga wakiltar kasarsa ta Ingila a  wasannin tamaula

 

Rooney da bayan kammala gasar Firimiya na badi, Manchester United ta sayar da shi ga Everton bayan shafe shekaru 13 a kungiyar, ya bayyana niyyarsa na ajiye bugawa Ingila ne bayan da kocin Ingila, Southgate ya sanar da shi cewa yana daga cikin wadanda ya zaba don su wakilci kasar a wasan da za su buga da Malta

 

Rooney ya yi godiya bisa ga damar da Southgate ya bashi, amma sai ya nuna cewa yana da bukatar ya mayar da hankalinsa kadai a bugawa Everton don ya taimakawa kungiyar da a nan ne ya fara tashe kai wa ga nasara

 

Rooney ya bugawa Ingila wasanni 119 kuma ya zura kwallaye 53, wanda hakan ya zama shi ne dan wasan da ya fi zurawa kasar Ingila kwallo a tarihi

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...