Yadda Ya Dace Musulmi Ya Fuskanci 10 Farkon Dhul-Hijjah

0 79

A yau Laraba ne aka shiga daya daga cikin watannin alfarma da Allah Ta’ala ya fifita wato watan Zul Hijja. Allah Ta’ala ya fifita ibadu a wasu wurare, kwanaki da lokuta a cikin wannan watan domin bawa ya samu dacewa da rahamarsa.

Allah ya fifita kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijja da abubuwa Kamar haka:

1. Allah Ta’ala Ya yi rantsuwa da su inda yake cewa: “Ina rantsuwa da Alfijir. Da darare goma” Suratu al-Fajr aya ta 1 da ta 2.
Imam Ibn Kathir, Rahimahullah, ya ce: Daruruwa goma da aka ambata a ayan su ne yinnai goma na farkon watan Dhul-Hijja. A duba Tafsiru al-Qur’anil al-‘azeem 8/390.

2. Yinnai goma na farkon watan Dhul-Hijja su ne mafi alheri yinnai na duniya.
An karbo daga Jabir, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Lallai Manzon Allah, Sallallahu’ alaihi wa sallama, ya ce: Mafi alherin yinnan duniya su ne kwanaki goma, yana nufin na Dhul-Hijja, sai aka ce masa: koda kwatankwacinsu da mutum ya fita jihadi domin Allah?.
Sai ya ce: “koda kwatankwacinsu ga wanda ya fita jihadi domin Allah, sai dai mutumin da akan turbutse fuskansa da kasa (wato ya yi shahada)” Sahihu al-Jaami’u al-Sagir 1133.

3. A cikin su Allah Ta’ala Ya yi umurni da a ambace Shi.
Allah Ta’ala Ya ce: ” Kuma su ambaci Allah a cikin ‘yan kwanuka sanannu”. Suratul Hajj 27.
An samo hadisi daga Abdullahi Bn Umar Radhiyallahu anhu, ya ce: “Manzon Allah, ﷺ, ya ce ‘Babu wasu yinnai mafi girma a wurin Allah kuma mafi soyuwa gare Shi da yake so a yi aiki a cikin su kamar wadannan yinnai goma, don haka idan sun zo ku yawaita fadin laa ilaaha illallahu, Allahu Akbar da Alhamdulillahi a cikin su”. Imam Ahmad ya ruwaito a cikin Musnad din shi 2/75.

4. A cikin wadannan kwanaki ne ake samun ranar Arafa. Wanda a cikin shi ne Allah Ta’ala Ya ke yawan ‘yanta bayi daga wuta.
An samo hadisi daga uwar Muminai A’isha, Radhiyallahu anha, ta ce: Manzon Allah, Sallallahu’ alaihi wa sallama, ya ce: “Babu ranar da Allah Ya ke ‘yanta bawa daga wuta kamar ranar Arafa, domin Allah Yana kusantowa sannan ya yi ma Mala’iku alfahari (da mutanen da suke filin Arafa) sannan ya ce: me wadannan suke nufi?” . Muslim ne ya ruwaito 1348.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...