Hoto: Dan Sanda 1 Ya Rasu, Mutane 11 Sun Jikkata a Sabon Harin Kunar Bakin Wake a Maiduguri

0 109

Rundunar ‘yan sandan jahar Borno ta ce mutane biyu sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon harin kunar bakin wake da aka kai a garejin muna da ke Maiduguri a jiya.

Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakain jami’in hulda da jama’a na rundunar, Murtala Ibrahim.

Sanarwar ta bayyana cewa dan kunan bakin waken ya doshi wata motar SARS, inda aka yi yunkurin harbe shi, lamarin da ya sa bom din ya tashi.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 1:45 na ranar jiya Laraba.

Bom din ya kashe dan kunar bakin waken tare da dan sanda daya, sai ‘yan sanda hudu da suka jikkata da kuma wasu mutanen guda 7.

An kwantar da wadanda suka jikkata a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inji sanarwar.

Ga hotunan bayan haren a kasa:

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...