Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa… Cr7 da Messi na shirin juyawa La Liga baya

0 585

 

Hukomomi a kungiyar Manchester City sun gana da mahaifin Leo Messi, Jorge Messi kan batun yiwuwar komawarsa Man City da murza leda. Sai dai labarin da ke ishemu shi ne, batun da ya fi karfi, shi ne barin Barcelona ga Messi ba zai yiwu ba a bana sai ko zuwa kakar badi

 

Watakila zuwa mako mai zuwa Cristiano Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa wata kungiya da bai bayyana ba zuwa yanzu. Dan wasan dai ya damu kwarai da dakatarwar wasanni biyar da aka bashi saboda hankade alkalin wasan da ya daga masa jan kati a karawarsu da Barcelona

 

 

Philippe Coutinho zai dauki matakin gabatar da wata hira da manema labarai don bayyana rashin jin dadinsa game da yadda Liverpool ke kokarin dakile barinsa kungiyar

 

Inter Milan ta mika bukatarta na daukar dan wasan baya na Arsenal, Shkodran Mustafi mai shekaru 25 a matsayin aro na shekara guda, inda daga bisani kuma za ta saye shi akan fam miliyan 20

 

Jonny Evans na West Brom zai kammala komawa Manchester City a mako mai zuwa a wani ciniki na fam miliyan 30

 

 

Tsohon dan wasan gaba na Manchester City, Steven Jovetic ya ki amincewa da tayin da Brighton ta yi masa na ya bar Inter Milan ta dawo gidanta da wasa

 

Tottenham za ta sake mika wani sabon tayi ga Lazio don daukar Keita Balde Diao mai shekaru 22 duk kuwa da cewa Juventus sun yi babban yunkurin daukar dan wasan

 

Juventus da Liverpool na rige-rigen daukar dan bayan Shalke da Jamus, Benedikt Howedes. Sai dai Howedes ya ce bashi da niyyar barin Schalke a bana

 

 

PSG za ta leka Napoli don zabare mai tsaron gidanta Pepe Reina mai shekaru 34

 

Neman Willian na Chelsea da Liverpool ta fara yi na nuna alamun cewa ta saduda Coutinho zai tafi

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...