Jihar Legas Ta Yi Odar Buhunan Shinkafa Tireloli 70 Don Bikin Sallah

0 62

Rahoto daga Premium Times ta bayyana cewa gwamnatin jihar Legas ta yi odar buhunan shinkafa har tireloli 70 domin siyarwa mutanen jihar don bikin Sallah.

Za a fara siyar da Shinkafar ne a yau har sai bayan Sallah.

Toyin Suarau, Kwamishinan ayyukkan noma na jihar Legas ya ce gwamnati za ta siyar da shinkafar a duk kananan hukumomin dake jihar kuma za a siyar da babban buhu 50Kg akan Naira 12,000, 25Kg akan Naira 6,000, 10Kg akan Naira 2,500.

Toyin ya ce gwamnati tayi haka ne don ta tallafawa musulmai domin yin bikin sallah inda gwamnati ta kara bunkasa kamfanin sarrafa shinkafa na “Rice milling plant” dake jihar Legas.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...