Magu Na Kokarin Gurgunta Shirin Yaki Da Cin Hanci – Ministan Shara’a

0 117

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya zargi Shugaban Hukumar yaki da rashawa (EFCC) Ibrahim Magu da kokarin gurgunta shirin da gwamnatin tarayya ke yi na kawo karshen cin hanci da rashawa a Nijeriya ta hanyar amfani da bayanan sirri ba bisa ka’ida ba.

Salihu Usman, Wanda shine Kakakin Ministan ya ce yadda Magu ke sarrafa bayanan sirri ya janyo aka cire Nijeriya daga cikin kasashen kungiyar nan dake kare bayanan sirri na kasa da kasa wato ‘Egmont Group’.

Tun ba a yau ba takun-tsaka ke tsakanin Ministan Shara’a da Shugaban EFCC bayan da Magu ya ki mikawa Ministan rahoton zargin rashawa da ake yi akan wasu tsoffin gwamnoni.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...