Ta Maka Iyayenta a Kotu Tare da Neman Diyyar Makuden Kudade Bisa Zarginsu da Harbinta da Muni

0 334

 

Wata mace ‘yar shekaru 44 a jihar California a kasar Amurka mai suna Annabelle Jefferson ta gurfanar da iyayenta, Robert da Ruby Jefferson a gaban kuliya tare da neman diyyar dalar Amurka miliyan 2 wai don su saka mata kwayoyin halittar muni, lamarin da ya saka aka haifeta da muni

 

Annabelle ta zargi iyayen da saka mata muni wanda ya yi sanadin mutuwar aurenta har sau uku tare kuma da jefa ta cikin halin kunci da takaici

 

“A lokacin da aure na fari zai mutu, tsohon mijina ya fadawa alkalin cewa a duk safiya in ya tashi ya ga fuskata sai ya ji kamar ya yi amai. Kai wani lokaci ma sai ya ruga zuwa ban daki don ya haras. Wannan ne dalilin da ya sa ya sake ni. Iyayena munana ne na a buga a jarida, a saboda haka bai kamata a ce su haifi ‘ya’ya ba. Ban ga wani dalilai da zai sa a basu dama su hayayyafa ba.”

 

 

“Mijina na biyu kuwa makaho ne, amma bayan an yi masa aiki a idonsa sai ganinsa ya dawo da akalla kaso 40 cikin 100. Shi ma ya sake ni mako guda kacal da ya fara gani,” inji Annabelle

 

Wannan lamari ne fa ya sanya Annabelle ta tuntubi mutane masu irin matsalarta, inda anan ne aka bata shawarar ta yi karar iyayen nata

 

Annabelle har ila yau na so ta yi amfani da damar da ta ke da ita a kotu na jan hankalin gwamnati da ta kirkiri wata doka za ta hana auren mace da miji har sai sun cika wasu sharuda na kyan jiki da na fuska

Annabelle
Iyayen Annabelle

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...