‘Yan Nijeriya Sun Bayyana Ra’ayoyinsu Game Da Batun Beraye a Ofishin Buhari

0 128

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya janyo cecekuce a Nijeriya bayan da ya yi ikirarin cewa beraye sun lalata Ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a don haka shugaban zai na aikinsa daga gida.

Buhari dai ya koma aiki ne a ranar Litinin da ta gabata bayan da ya dawo gida Nijeriya daga hutun jinta da ya yi a birnin London wanda ya shafe kwanaki 103.

Sai dai komawar shi aiki ke da wuta sai masu taimaka masa akan harkokin yada labarai suka tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa shugaban zai na aiki ne daga ofishinsa na gida.

Duk da cewa wannan magana ba ta yi wa wasu ‘yan Nijeriya dadi ba, ba ta haifar da cecekuce ba har sai da Garba Shehu ya bayyana dalilin aikin shugaban a gida da cewar beraye da kwari ne suka yi wa Ofishin shugaban illa.

‘Yan Nijeriya da dama sun fito a kafafen sada zumunta inda da dama suka nuna cewa akwai alamar tambaya a wannan batu.

Yayin da wasu ke ganin karya ce kawai ta rainin hankali, wasu gani suke yi ana yunkurin boye yiwuwar cewa shugaban bai gama warkewa ba ne ga ‘yan Nijeriya.

Kai har ma akwai wadanda suka yi kira da a kori Garba Shehu daga aiki saboda irin wannan magana ba ta dace ba.

Wani mai amfani da shafin Twitter haka ya ce “Shin Garba Shehu bai san cewar wannan karyar ba ta zauna daidai ba a yayin da yake rubuta sanarwar shi?”

Wani kuwa haka ya ce “Tabbas wannan batun berayen zai jawo hankalin duniya…”

Tsohuwar ministar ilimi Oby Ezekwesili kuwa haka ta ce “Na yi duban nutsuwa akan wannan batu na beraye, babu kanshin gaskiya a ciki. An Karawa beraye girma kawai”

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...