Jaruman Kannywood Sun Samu Lambobin Yabo a Bikin Karramawa na ‘City People’

0 158

A bikin karramawa na ‘City People’ na wannan shekarar, kamar yadda aka saba ba a bar Kannywood a baya ba.

Bikin wanda aka yi a ranar 8 ga watan Oktoba a dakin taro na ‘Baltimore Event Center’ da ke Oregun Ikeja a jahar Lagos ya karrama jiga jigai da jarumai masu tasowa bangaren shirya fina-finai a Nijeriya.

Aminu Momo shi ya lashe kambun jarumin jarumai, yayin da Lawal Ahmed ya lashe na mataimakin babban jarumi.

KARANTA WANNAN: Zan tsaya takarar dan majalisa a 2019 – Lawal Ahmed

Ali Nuhu ya samu kambun fuskar Kannywood 2017, yayin da dan shi ya lashe kambun jarumin jarumai a fannin kananan yara.

Sauran wadanda suka samu lambar yabo sun hada da Ibrahim Daddy, Hajara Isah, Kamal S. Alkali da ya lashe kambun daraktan daraktoci, da Sani Sule Katsina a bangaren furodusoshi.

You might also like More from author

Comments

Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...