Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Abinci Kala 5 Da Ke Rage Kaifin Hawan Jini

0 483

Duk da cewa hawan jini na daya daga cikin cutututtukan da suka zama ruwan dare a cikin jama’a, mutane da dama ba su san cewa akwai nau’ikan abinci da za su ci wadanda za su taimaka wajen rage kaifin shi ba:

A yau Al’ummata na tafe muku da irin wadannan nau’ikan abinci guda 5 wadanda ba su da wuyar samu, kuma kowa zai iya saya, ga su kamar haka:

Madarar shanu

Madarar shanu na dauke da sinadaran calcium da Vitamin D wadanda idan suka hadu guri daya ke taimakawa wajen rage hauhawan jin da kaso 3 zuwa 10.

Kwai

Ruwan kwai bayan an tsame kwanduwa ya na cike da sinadarin Protein, Vitamin D da sauran su. Wadannan sinadarai na taimakawa wajen rage yawan hawan jini.

KARANTA WADANNAN: Shan zobo ya na maganin hawan jini – Masana

Ayaba

Ayaba cike ta ke da sinadarin Potassium. Ya na da kyau mai hawan jini ya na kara ta a cikin abincin sa ko kuma ya ci ta tare da kyau dafaffe a matsayin karin safe.

Cakulet

Bakin cakulet ya na dauke da sinadaran Falvonols wadanda ke karawa jijiyoyi taushi. Ya na da kyau mai hawan jini ya jimiri cin sa musammam ma wanda aka hada da akalla kaso 70 na cocoa.

Man Zaitun

Ya na daya daga cikin mayukan da ba su da hatsari ga jiki. Ya na dauke da sinadarin Polyphenols wanda ke taimakawa wajen rage ciwon hawan jini.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...