Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Abubuwan Da Kiristoci Za Su Iya Koya Daga Wajen Musulmai – Pulse.ng

0 461

Mujallar yanar gizo ta Pulse.ng ta wallafa jerin wasu abubuwa da ta hakikance kiristoci a duk fadin duniya za su iya koya daga wajen musulmai don kyautata alakarsu da Mahaliccinsu

Mujallar ta ce duk da cewa a lokuta da dama addinan biyu na ganin baiken juna wajen yadda mabiya ke gabatar da akidu da tanade-tanaden addinansu, marubucin ya ce, wannan ba dalili bane na Kiristoci su ki koyon kyawawan dabi’un musulmi

 

Misalan abubuwan da Kiristoci ya kamata su dauka a matsayin darasi daga wajen Musulmai sun hada da:

Tsai Da Sallah Da Daukarta Da Muhimmanci

Musulmi a duk fadin duniya na da wata shaida ta daukar ibadar sallah da matukar muhimmanci. Duk da kasancewa ibadah ce da ke bukatar duk wani baligi mai hankali da ya ke cikin tsarki ya gabatar da salloli biyar a duk ranar duniya, Musulmai ba sa kasa a gwiwa wajen gabatar da wannan ibadar. Wannan mayar da hankali wajen gabatar da nau’in ibada don samun kusaci da Allah wani abu ne da Kiristoci ya kamata su koya daga musulmi ba wai kawai su mayar da addininsu na mako-mako ba

Baiwa Ibadar Azumi Muhimmanci

Kodayake akwai azumi a addinin Kirista, amma sam mabiya addinin ba su dauke shi da muhimmanci ba domin sai mutum ya ga dama zai yi, kuma iya adadin da ya ga dama zai yi ba tare da ya rama ba. Wannan ba haka ya ke ba a musulunci. Musulmai na gabatar da azumin watan Ramadana a matsayin wajibi ga baligi sai dai wanda shari’a ta daukewa. Wannan shima wani abu ne da ya kamara Kiristoci su dauka daga Musulmi

Bayar Da Zakka

Zakka na daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar. Musulmi ya dauki wannan nau’i na ibada da muhimmanci, musamman ma zakkan fidda kai. Wannan tsari na bayar da zakka yana taimakawa wajen dinke gibin da ke tsakanin masu shi da marasa shi. Kiristoci ma ya kamata su kwaikwayi musulmi wajen bayar da zakka

Mika Wuya Tare Da Bin Dokokin Allah Sau Da Kafa

Kowane tsaka-tsakin musulmi yana kokari wajen ganin ya kiyaye dokokin Allah sau da kafa iya iyawarsa. Ko shakka babu za ka samu wani ya fi wani takawa da tsoron Allah, amma za ka samu musulmi na nuna mika wuyansa cikin Tauhidi tare da kokarin kaucewa haramun iya iyawarsa

Sutarce Al’aura

Wani abu da musulmi shi ne, sun san daga inda al’auarar dan adam ya fara kuma gwanaye ne wajen suturce wannan bangare na jiki. Matan musulmi za ka samesu akalla sanye da mayafi, in har ba za su sanya hijabi ko himar ba. Wasu daga matan musulmi har nikab suke sanyawa wanda ba haka abin ya ke ba a wajen kiristoci inda da dama suke da ra’ayin cewa wai babu ruwan Ubangiji da yanayin suturarka

 

Marubucin ya ci gaba da cewa kodayake ni ba musulmi bane, ni kirista mai alfahari da addininsa, amma maganar gaskiya ita ce musulmi sun fi mu kiyaye hakkokin mahalicci, wannan kuma ya kamata mu koya daga wajensu don kaiwa ga samun tsira a gobe
Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...