Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Adam A Zango Ya Caba Masoyanshi Da Kyaututtuka

0 398

Shahararren jarumin Kannywood, Adam A. Zango ya baiwa masoyanshi da suka halarci kaddamar da sabon fim din shi mai suna Gwaska Returns Kyaututtuka na musamman.

An kaddamar da fim din ne a Ado Bayero Mall dake jahar Kano a ranar Talatar da ta gabata, 12 ga watan nan.

Bikin kaddamarwar ya samu halartar jiga-jigan Kannywood kamar su Nafisa Abdullahi, Ali Nuhu, Ado Gwanja, Nura M Inuwa, Fati Abubakar da sauransu.

Zango ya bayarda kyaututtukan riguna, agoguna da sauransu ga manyan masoyan shi.

A hira da ya yi da jaridar Premium Times, daya daga cikin wadanda suka halarci bikin, Mansoor makeup ya bayyana cewa wannan abu da Zango ya yi abu ne da ba a taba yin irin shi ba a Kannywood. Ya ce wannan abu ya nuna cewa ya dauki masoyanshi da muhimmanci.

A wani bidiyo da Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya godewa abokan aikin shi da suka amsa gayyatar shi sannan ya yi alkawarin zai ci gaba da karrama masoyan shi na hakikan.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...