Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Agwaluma Na Taimakawa Wajen Magance Zazzabin Malaria Mai Naci – Binciken Kimiyya

0 527

Wani sabon binciken kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani.

Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.

Masu binciken wadanda ‘yan Nijeriya ne sun gwada ingancin maganin a akan beraye da ke dauke da cutar, idan aka samu nasarar magance ta daga jikin su.

Masanan sun ce a nan gaba akwai yiwuwar za a koma amfani da saiwar Agwaluma da ganyayyakin ta wajen hada magungunan Malaria.

KARANTA WANNAN: Sama da mata miliyan 15 ke zubar da ciki a duk shekara – Bincike

Izuwa yanzu, magungunan malaria da aka sani na kara rage karfi a yayin da suke daina aiki akan kwayoyin cutar nau’ika daban daban, wanda ba karamin koma baya bane ga yunkurin kakkabe cutar a fadin duniya.

 

Masu binciken sun ce wannan ne ya sa dole ne a fito da wasu hanyoyi na daban na magance cutar a cikin gaggawa, inda kuma amfani da Agwaluma na daya daga cikin irin wadannan hanyoyi.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...