Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Alfanu Da Rashin Alfanun Aske Gashin Gaba Ga Mata – Binciken Lafiya

0 4,475

Akalla kaso 84 na matan duniya da suka isa mallakar gashin gaba na aske gashin gaban nasu kamar yadda wani bincike na shekarar 2016 da aka wallafa a mujallar JAMA da ke wallafa mukaloli da suka shafi kiwon lafiyar fata

 

Binciken ya bayyana cewa mafi yawan mata na yin wannan aski ne da kansu ta hanyar yin amfani da abubuwa masu kaifi a bangaren jikinsu da ke da mafi raunin kwari, wanda hakan zai iya haifar da rauni ko kurarraji, ko kujewa, ko dai wani illa ga wannan bangare na jiki

 

An tambayi wata kwarrariyar likitar fata, Michelle Metz, mene ne alfanu ko illar aske gashin gaba?

 

Sai ta ce “Wannan ya danganta da ra’ayin mace na ko tana so ta aske gashin gabanta ko kuma tana so ta bar shi. Sai dai akwai abubuwa biyu da zan iya kira da hatsarin aske gashin gaba ga ‘ya mac

 

Da farko dai in ki ka kasance kina aske gashin gabanki a kai-a kai, to akwai yiwuwar kamuwa da lalurar folliculitis. Folliculitis kuwa lalura ce da ke kama kafar gashi ta yadda kafar gashin zai kumbura ya yi ta kaikayi da radadi. Yawanci matan da ke amfani da reza na cikin barazanar kamuwa da wannan cuta. Kuma in suka samu cutar, za su shiga sosa gabansu a kowane lokaci musamman in sun dan yi zufa a wannan wuri. Ga wacce ke fama da wannan lalura a halin yanzu, to ta nemi kwayar (anti-biotic)

 

A kan samu kuma wani lokaci kaifin abin askin ya sanya silin gashin a maimakon ya tsiro zuwa waje, sai ya koma yana tsiro ta ciki, wanda shima wannan yawan aske gashin gaba ke haifar da shi. In aka samu irin wannan, ya ka janyo mace ta zama ta rasa nutsuwarta a lokuta da dama sakamakon kumburi da jikinta kafar gashin zai yi tare da haifar mata da radadi da kaikayi maras misali (ga wacce ke fama da wannan lalura a yanzu, to ta gwada shafa man OTC hydrocortisone don samun lafiya)

 

Ya kamata mu fahimci cewa akwai dalilin da yasa Mahaliccinmu ya hukunta tsirowar gashi a gabanmu a lokacin da girma ya zo mana. Gashin gaba yana da amfani matuka wajen kare farji daga illar da gautsin suturar da muke sanyawa ke yi mana na gugar gabanmu babu kakkautawa. Kasancewa fatar gabanmu ba ta da kwari kamar na sauran bangarorin jikinmu, gashin gaba na ba shi kariya daga yagewa ko fashewa ko kujewa sakamakon guga ko haduwa da wani abu mai karfi bisa karamin hatsari

 

Gashin gaba na hana saukar ni’imar da muke fitarwa a yayi jima’i da ma maniyyin da ya ke gangarowa daga cikin farji a lokacin jima’i zuwa shimfidarmu. Gashin gaba ne ke tsane shi tare da hana shi gangarawa cikin sauki zuwa kan shimfida

 

A saboda haka nake jan hankalinmu da a maimakon mu aske gashin gaba daya ta hanyar debe sumar tadai-tadai, kamata ya yi a ce mu yi saisaye gashin gaba don gudun yi wa fatar gabanmu da ma gaban namu illa

daga cikin illar aske gashin gaba

Da dama dai mata kan aske gabansu ne dama saboda zufa da da sumar ke haifarwa a gabansu, wanda ke haifar da dauda ga wando da kuma matse-matsi. Sai kuma wani dalilin shi ne, ma’aurata na yin aski ne saboda mazajensu sun fi sha’awar su ga gaban matan nasu babu suma

 

A takaice dai in har ya zama dole sai kin yi askin gashin gabanki, to ki yi shi sanye da dan kamfe a jikinki, ta yadda za ki aski duk wata suma da ke kasan dan kanfan, Ala basshi sumar da ke kusa da farji, sai a saka almakashi a yanke shi

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...