Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Allah Ya Yiwa Tsohon Alkalin-Alkalai Yusuf Rasuwa

Allah Ya Yiwa Tsohon Alkalin-Alkalai Yusuf Rasuwa

0 130

Allah ya yiwa tsohon alkalin alkalai na jihar Kwara da kuma shugaban kungiyar masarautan Ilorin (IEDPU) , mai shari’a Saka Yusuf (mai ritaya) rasuwa.

 

Marigayin ya rasuwa ne a ranar Litinin  12 ga watan Fabrairu 2018 da daddare bayan ya kamu da wani rashin lafiya.

 

Karanta wannan: Dubban Jama’a Sun Sauya Sheka Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC A Kwara

Shugaban majalisar dattijai na kasan Nijeriya, Santa Bukola Saraki, ya tabbatar da rasuwan a shafinsa na Twitter.

 

Saraki ya ruwaito kamar haka, “Ina yiwa iyalan marigayi mai shari’a Saka Yusuf wanda ya rasu a yau ta’azziya.

 

Karanta wannan: Wani Dan Nijeriya Ya Yi Alkawarin Biyan Duk Wanda Ya Yi Rajistar Zabe Wasu Adadin Kudade

 

“Mai shari’a Saka ya kasance mutum mai ilimin a bangaren shari’a , wanda yayi aiki a karkashin na a lokacin da ne ke gwamna a jihar Kwara.

 

“Mai shari’a Saka ya bada na shi gudunmawa a harkokin shari’ar wanda ba za a iya mantawa ba, babu shakka za mu ji kewansa. Allah ya jikan shi da rahama.”

 

Karanta wannan: Sojoji Sun Kwato Mutane 46 Daga Hannun Boko Haram Bayan Sun Kakkabe Sansanin Sabil Huda

 

 

Za’a binne marigayin a gidansa da ke GRA a birnin Ilorin a misalin karfe 10 na safe.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...