Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Ana Shan Kwalaben Codein Fiye da Miliyan 3 a Kowacce Rana a Jahohin Kano da Jigawa – Majalisa

0 549

Majalisar dattawan Nijeriya ta nuna damuwar ta game da yadda kwankwadar kayan maye ya zama ruwan dare a jahohi 19 na Arewacin kasar nan.

A wani kudiri da dan majalisa mai wakiltar jahar Borno mai suna Sanata Baba Kaka Bashir Garbai tare da wasu sauran ‘yan majalisa 37 suka gabatar a zauren, an bayyana adadin kwalaben codein da ake kwankwada a jahohin Kano da Jigawa kadai a matsayin miliyan uku da doriya a kowacce rana ta Allah.

Majalisar ta ce a jahohi 19 na Arewacin kasar nan, matan aure da ‘yan mata da ke makaratun gaba da sakandire, mata masu aiki da marasa aiki da rikicin Boko Haram ya tarwatsa suna daga cikin wadanda ke fama da shan kayan maye.

Haka zalika majalisar ta ce ba a bar yaran ‘yan makarantun sakandire a baya ba.

KARANTA WANNAN: Wasu ‘yan bautan kasa sun gamu da ajalinsu a jahar Adamawa

A don haka ne majalisar ta bukaci kwamitocin ta da ke kula da harkokin miyagun kwayoyi da kiwon lafiya da su yi bincike akan batun su gabatar da sakamakon su ga majalisar domin ta san irin dokar da za ta kafa.

Majalisar ta kuma bukacin gwamnatin tarayya da ta hada hannu da karfe da masu ruwa da tsaki; gwamnatocin jahohi, da na kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, hukumar hada magunguna a Nijeriya da kungiyoyi masu zaman kansu domin afitar da hanya mafi inganci da za a yaki wannan tarzoma.

Haka kuma ta bukaci ma’aikatar kiwon lafiya da ta samar da gurare na musamman da za a na yi wa masu harka da miyagun kwayoyin magani, tare da umartar hukumar NAFDAC da ta shiga wayar da kan jama’a akan illolin da ke tattare da abun.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...