Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Babu Wani Aibin Dake Tare Da Ficewar Atiku APC – Ibrahim Babangida

0 221

Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB, ya bayyana cewa babu wani  yi aibin dake tattare da ficewar Atiku daga Jam’iyya APC zuwa Jam’iyyar PDP tunda dokar kasa ta bashi damar yin haka.

Babangida ya bayyana haka a yayin wata ziyara da manyan jiga jigan PDP suka kai masa a gidansa dake birnin Minna a jihar Neja inda yake cewa Atiku Abubukar dai dan Nijeriya kuma dan siyasa dake da damar ficewa da shiga duk wani jam’iyyar da ga dama bisa yadda dokar kasa ta tanada.

BUDE: Mata Ta Zubawa Mijinta Tafasasshen Ruwan Zafi (Hoto)

Tsohon shugaban ya yi kira ga manyan jiga jigan PDP dasu mayar da hankalinsu wajen babban taron kasa da jam’yyar ke kokarin shiryawa ranar Asabar mai zuwa. Ya ce, yana mai musu fatan alkhairi kuma Allah yasa ayi taro lafiya, a kuma tashi lafiya.

Dangane da komawar Alhaji Atiku Abubakar jam’iyyar PDP, Janar Babangida ya kara cewa tsarin mulkin kasa ya bashi hurumin yin hakan tare da iya shiga kowace jam’iyya. Inji tsohon shugaban kasar

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...