Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga ‘Yan Uwa Mata

0 1,349

Aure shi ne mafi girman al’amari a rayuwar ‘ya mace. Ta hanyarsa ne za ta samu damar yin cikakkiyar bauta ga Ubangijinta, sannan ta samu damar kafa nata iyalin.

 

Idan aure yayi jinkiri a gareki, kar ki yi amfani da wannan damar wajen biyan bukatar sha’awarki ta hanyoyin da Ubangijinki ya haramta.. A’a ki yi hakuri ki kama kanki. Ki dage wajen ibadah da neman yardar Ubangijinki.

 

Ki kyautata zato ga Ubangijinki. Shi mabuwayi ne mai hikima. Kuma duk abinda ya ƙaddara miki, to ki yi fatan Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, sannan ki nemi mafita a wajensa, ba wajen bokaye da ‘yan bori da ‘yan duba ba..

 

Zina da Maɗigo da kallon hotunan batsa, da yin chatting na batsa duk Kofofin samun tsinuwa ne da kuma fushin Ubangijinki.. Ki kyautata ma kiji tsoron Ubangijin da ya halicceki kar ki kai kanki ga halaka.

Buɗe Ka Karanta: Zikirai 7 Mafi Tsada A Rayuwar Musulmi

Idan ki ka aikata wani abu daga cikin wadannan, to kinci amanar kanki, Kin ci amanar iyayenki, kinci amanar dukkan ‘yan uwanki da danginki, kinci amanar ‘ya’yan da zaki haifa nan gaba…. Sannan Uwa-Uba kinci amanar ALLAH DA MANZONSA (SAWW).

 

WANNAN NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU, Mun rubuta ne domin isar da Sakon Allah da Manzonsa izuwa zukatan masu rabo. Allah yasa damu daku mu samu tsira a duniya da lahira. Allah shi kiyayemu daga ZINA da dukkan dangoginta. Ameen

 

Zauren Fiqhu

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...