Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Budurwa Ta Auri Saurayi Kwanaki 6 Bayan Da Haduwar Su A Shafin Facebook (Hotunan Bikin)

0 609

Wata tsaleliyyar budurwa, Chidimma Amedu, ta auri wani matashi da ta hadu da shi a shafin sada zumunta na Facebook. kwanaki 6.

 

Wannan abun ya faru ne bayan matashin ya tallata kan sa a shafinsa na Facebook a 39 ga Disamba 2017, inda ya bayyana cewa duk wacce za ta iya auren sa ta amsa shi.

 

Ina ya ce a shirye ya ke a daure ma su auren a 6 ga watan Junairu 2018.

 

Karanta wannan: Ba a Yankewa Masu Fyade Hukuncin Da Ya Dace Da Su – Aisha Buhari

 

“Na kai munzalin yin aure, sannan kuma a shirye ni ke a daura ma ni aure ba tare da bata wani lokaci ba.

 

Wacce neman auren ta tura da amincewar ta, wacce ta tafi cancanta zan aure ta kafin 6 ga watan Junairu 2018. Za a rufe kofar a misalin karfe 12:00 dare na 31/12/2017,” Chidimma ya ruwaito kamar haka a shafin na sa na Facebook

 

Daga sai ruwaito haka bayan ya tallata kan sa.

 

“Ba wasa ni ke yi ba fa sannan kada ku ce ba ku gani ba a cikin lokaci ba. Allah ya bada sa’a.”

 

Ya samu amsa daga wurin ‘yan mata da dama, amma wata budurwa, Sophy Ijeoma, tafi jan hankalin sa.

 

Karanta wannan: Gurɓacewar Tarbiyya: ‘Yar Shekaru 17 Ta Liƙa Hotunanta Tumɓir A Shafinta Na Facebook (Hotuna)

 

Ta amsa shi kamar “Ina sha’awar hakan, ka aika ma ni da sako na musamman mu tattauna.. lol,” ta saka a shafin na sa.

 

A farko, ta aza wasa ya kai, shi ya sa ta amsa masa.

 

Daga aikata mata sakon na musamman a shafin Facebook, bayan hakan sai ya kira ta ta yanar gizo a Facebook, kafin ku sani sai ga rayuwar ta ya dauke wani sabon sallo.

 

Karanta wannan: Yadda Za Ka Tsare Shafinka Na Facebook Daga Masu Kutse

 

Chidimma ya saka tallatawan a matsayin wasa ni amma Sophy na furta cewa tana da sha’awar yin aure shi ma ya fara samun sha’awar yin hakan.

 

Bayan kwanaki 2 da tattaunawa, ya yi tafiyar kilomita 500km (wanda yayi daidai da mil 300) daga inda ya ke zama a babban birnin tarayya Abuja zuwa garin Enugu a gabashin Nijeriya inda ta ke budurwar ke zama.

 

Tana ta jiransa a gaban wani shago, abunda dai kamar tatsuniya, “Muna gallarawa juna kallo muka fara son juna nan take” wato “Love at first sight”, haka ta kira shi.

 

karanta wannan: Facebook Ta Rufe Shafukan Mutane Dubu 10

 

“Babu wani namijin da ya kai shi haduwa a wuri na, a nan take na fara son sa.”

 

Bayan awani 2 da haduwan mu,  sai ya ce yana so ta hadu da kawun sa wanda ya kasance yana zama a garin Enugu.

 

Sai da ganan ya tambaye ta yaya ta ke gani? sai ta fada masa cewa hala wasa ya ke yi, amma kuma ta ji dadin jin hakan don ya ma ta.

 

“Sai mu ka tafi zuwa wurin kawu na, sai ya ce: ‘Kawu ga matar da ni ke so na aura nan.'”

 

Karanta wannan: Hukumar Kasan Zambia Ta Kama Wani Mutum Wanda Ya Zagi Shugaban Kasar A Facebook

 

Kamar yadda iyalan Chidimma ba su wasa wajen aiwatar abubuwa da suka shafi harkar aure, don kawun na sa a na take ya amince da yarinyar.

 

Masoyan sun dade suna kawance a shafin sada zumunta Facebook amma ba su taba magana da juna ba sai bayan da ya tallata kan sa.

 

Samun amincewa iyalan ka game da wacce mutum zai aure na daya daga cikin al’adun inyamurai.

 

Alhali kuwa, zabar matar aure a tallar shafin sada zumunta na Facebook tare da auren ta a cikin kwanaki 6 ba abunda za a iya amincewa da shi ba ne.

 

Karanta wannan: ‘Yan Sanda Sun Tsare Wani Dan Jarida Akan Sakon Da Ya Wallafa a Shafinsa Na Facebook

 

A wannan lokacin, a cikin soyayyar kwana 1, Sophy ta fara gane cewa lallai ba wasa Chidimma ya ke yi ba;  amma ya mutum zai iya auren soyayya da mutumin ya hadu yanzu yanzu?

 

Ta kasa fadin cewa ko ta sumbaci saurayin da aka masu baiko ba tukun, amma abunda ya bata mamaki shine kokari da hazakar sabon saurayin na ta.

 

“A farko da na gallara masa ido, ya ja hankali na, amma bansan cewa lallai dagaske aure na ya ke so yayi ba.

 

“Sai bayan da muka hadu da kawunsa da matarsa, shine lallai na yadda da cewa wata kila auren zai iya yuwuwa.”

 

Karanta wannan: Yakamata ‘Yan Matan Nijeriya Su Rage Lokacin Da Suke Batawa A Kan Facebook Da Instagram- Sarkin Musulmi

 

Zancen Baikon

 

Sai shiga cikin damuwa, aka bar ta da tunanin yadda za ta samu amincewar iyalanta na auren mutumin da ta hadu da shi a ta shafin sada zumunta na Facebook.

 

Amma suna da kwar jinin hakan a zukatan su. Bayan duk suna son juna da haduwar su na farko, ko kuma da aikawa juna sa sako, tare da samun amincewar kawun Chidimma, masoyar daga nan suka tafi zuwa ganin iyalan Sophy a wannan ranar.

 

Karanta wannan: Kamfanin Facebook Zai Dauki Ma’aikata 3000 a Fadin Duniya

 

Amincewar iyalan mutum na da muhummancin a al’adar inyamurai

.

Sophy ta bayyana yadda ta fadawa mahaifiyar labarin abunda ke faru. Mahaifinta ya dade da rasuwa, mahaifiyar na ta ta ce ba za ta iya yanke hukunci game da amincewa da auren ba, wuka da nama na hannun ‘yan uwan Sophy na amincewa da auren.

 

An ce matar mutum kabarinsa, babban yayan Sophy ya amince da su aure juna.

 

Karanta wannan: Facebook Zai Kirkiri Naurar Da Za Ta Iya Bayyana Abunda Mutum Ke Tunani a Rubuce

 

Bayan an yayan Sophy ya yiwa Chidimma wasu ‘yan tambayoyi – sai ya amince da shi, shikenan kawai Chidimma da Sophy sun yi baiko daga kuma za a daura masu aure a cikin kwanaki 6.

 

A shekarar da ta gabata, Chidimmma, yayi baiko da wata yarinya amma an daga bikin zuwa watan Disamba, amma sai suka rabu a watan Maris bayan ta fasa aurensa.

 

Ana shiga watan Disamba, kuncin rashin aure a wannan watan kamar yadda aka shirya a baya ya saka shi tallata kan sa, ya ce.

 

Karanta wannan: Mai Yin Sojan Gona Da Sunan HADIZA GABON A Dandalin Facebook Ta Shiga Hannu

 

Yadda Daurin Auren Ya Kasance

“Dama ina da niyyar yin aure, kuma na aje ranar a rai na, amma banda amarya, shi ya sa na wallafa wannan tallan a matsayin wasa, amma ban boye ba, na bayyana shi a fili.”

 

An tambaye Sophy ko ta san da batun baikon sa a baya ko wata kila yayi hakan ne don ya huce zafin abunda masoyiyarsa da aka masa baiko da ita ta masa da ita Sophy, amma Sophy ta yi watsi da wannan jawabin da aka ma ta.

 

“Duk wannan jawabin bai dame ni ba — idan ka ga abunda ka ke so, kada ka mutum ya bata lokaci kokarin samun shi.”

 

Sun dade suna kawance a shafin sadar da zumunta na Facebook fiye shekaru 1, amma ba su taba haduwa da magana da juna ba sai da ya wallafa wannan tallar.

 

Karanta wannan: Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg na Ziyara a Nijeriya

 

“Ina da sha’awar yin aure, ka tura ma ni da sako.. lols”  kawai ya hada su auren juna.

 

Sophy ta bayyana cewa kawayenta sun ta sukar abun, a yayin wasu daga cikin su ba su yadda da zancen ba, amma ta ce: “Idan mutum ya ga masoyinsa na asali, zai gane cewa shine”.

 

Karanta wannan: Facebook Zai Kirkira Hanyar Gano Masu Yunkurin Kashe Kansu

 

Kuna cikin farin ciki  bayan faruwar hakan?

 

Sunyi bikin gargajiyar su kamar yadda al’adar inyamurai ta shirya a 6 ga watan Junairu, sanna sun saka hotunan bikin na a shafukansu na Facebook — duk da cewa abun na ba mutane da ke bisa kan yanar gizo mamaki.

 

A farko dai Chidimma ya wallafa tallar kansa da wasa amma daga baya abun wasa ya koma dagaske.

 

Kamar yadda ku ka sani ne jama’a za su magana a kan lamarin, amma mutane da dama sun marawa masoyan baya.

 

Karanta wannan: Shafin Facebook Zai Samar Da Yanar Gizo A Afirka

 

They hope to have a church wedding in April and perhaps a honeymoon somewhere nice, he said. Nan

Ana sa ran za su gudunar da bikin cocin su a wata Afrilu sannan kuma wata kila za fita yawon shakatawa (honeymoon irin na sabbin ma’aurata.

 

Lallai wannan shi ake kira da SOYAYYAR FACEBOOK.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...