Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

An Bukaci Majalisun Kananan Hukumomi Da Su Rinka Bin Tanadi-Tanaden Kasafin Kudi Sau Da Kafa

0 79

Shugaban kwamatin kula da kananan hukumomin na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Husaini Kadeta yayi kira ga majalisun kananan hukumomin jihar jigawa da su rinka bin tanadi-tanaden kasafin kudi sau da kafa domin kawo ci gaban rayuwa a yankunan kananan hukumominsu.

 

Karanta wannan: Yara Mata 4 Sun Nitse a Ruwa a Jahar Jigawa, a Yayin Debo Itace

Yayi wannan kiran ne lokacin tantance kudurin kasafin kudin 2018 na k/h Guri, inda ya bayyana kundin kasafin kudin a matsayin jagora wajen aiwatar da tanadi-tanaden da aka yi wa jama’a.

 

Karanta wannan: Gwamnatin Jihar Jigawa Za Ta Dauki Sabbin Malamai 5,000 A Wannan Shekarar

A nasa bangaren, wakili a kwamatin Alhaji Adamu Idris Andaza ya bukaci kananan hukumomin su rubanya kokari wajen tattara kudaden shiga tare da amfani da dabarun tattara kudaden shiga na GEMS-3 domin cimma nasarar dake bukata.

 

Karanta wannan: Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 15 a Jigawa

Da yake kare kasafin kudin karamar hukumarsa, shugaban k/h Guri Alhaji Jaji Adiyani yace sun kiyasta kashe fiye da naira miliyan 1 da miliyan 868, inda naira miliyan 477 za su tafi ga manyan ayyuka.

 

Karanta wannan: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu ‘Yan Fashi Da Makami 4 A Jihar Jigawa

Yace za su gina sabuwar Abatuwa da magudanan ruwa da kuma yin jinga dan kaucewa ambaliyar ruwa a cikin Guri da sayo magungunan dabbobi da dashen bishiyoyi a gefen hanyoyi da sanya hasken wutar lantarki a wasu garuruwa.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...