Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Charlyboy Ya Kira ‘Yan Siyasa Da Fastoci Masu Mallakar Jiragen Kansu “‘Yan Banza”

0 675

Mawaki sannan kuma mai fafutika, Charles Oputa, wanda aka fi sani da suna Charlyboy, ya kira duk wasu ‘yan siyasa da fastocin da suka mallaki jiragen saman mallakar kan su a matsayin ”yan banza”.

 

Karanta wannan: ‘Yan Kungiyar Sirri Sun Kashe Wani Fasto A Legas

 

Shahararren mawakin ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke Allah waddai da halin da kamfanin sufurar jiragen saman mallakar kasan Nijeriya wato Nigerian Airways ke ciki.

 

Karanta wannan: Charlyboy Ya Gurfanar Da Rundunar ‘Yan Sanda a Kotu, Ya Na Bukatar a Biya Shi Diyyar Naira Miliyan 500

 

A wani rubutu da yayi a shafinsa na Twitter, shugaban kungiyar fafutika na OurMuMuDonDo, ya saka hotunan jiragen sufurar sauran kasashe da na kasar Nijeriya wato Nigerian Airways.

 

Karanta wannan: Fastocin Takarar Abdulrasheed Maina Sun Bullo a Kaduna Da Abuja (hoto)

 

Ya ruwaito kamar haka: “Wannan abun kunya ne, Nijeriya ba ta da jiragen saman daukan kayayyaki na kan ta amma akwai jiragen sama 100 wanda ‘yan siyasa (barayin gwamnati, da masu kudin kasa) da kuma fastoci wadanda suke kiran kan su limamen mujami’suka mallaka masu zaman kansu.

 

Karanta wannan: Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Buhari Ba Zai Yi Murabus Ba

 

“Allah ya sa juyin juya halin ya ci karfin ‘yan banza.”

 

A wani bincike da kafafen yada labarai na Dailypost ta yi ta gano cewa an kafa kafanin jiragen saman Nijeriya wato Nigerian Airways Ltd a shekarar 1958 bayan an rusa kamfanin sufurar jiragen saman nahiyar Afirka ta Yamma (WAAC). Ana kiransa da sunan WAAC Nijeriya kafin a canza masa suna zuna Nierian Airways a shekarar 1971. A kulle kamfanin a shekarar 2003.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...