Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

“Da Gurbatattun ‘Yan Kannywood Na Ke Rigima, Ba Da Ali Nuhu Ba -Inji Adam Zango

"Da Gurbatattun 'Yan Kannywood Na Ke Rigima, Ba Da Ali Nuhu Ba -Inji Adam Zango

0 838

Fitaccen jarumin fina-finai hausa kuma mawaki dan asalin jihar Kaduna Adam A.Zango ya bayyana cewa shi ba da abokin aikin shi Ali Nuhu yake rigima kamar yadda wasu ke zato ba.

Jarumin wanda ke cin gashin sabon shirin fim da ya fitar kwanan baya mai take “Gwaska Returns” yana mai koke wajen kwato hakkin sauran abokan aikinsa.

Kamar yadda ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta ta Instagram, jarumin ya mayar da akalar fushinsa ga gurbatatun yan kannywood masu ruwa da tsaki game da miyagun ayyukan da suke yi na rashin adalci da bayar da cikakakken hakkin jama’ a. Ya bayyana kamar haka;

“Ni ba da Ali Nuhu Nike rigima ba. Da gurbatatun yan Kannywood nike rigima, wadanda basu da yardar Allah. Wadanda sai Ali Nuhu da Adam A.Zango kadai suke iya sakawa a fim. Wadanda suke danne hakkin iyayen mu jarumai idan suka saka su a fim. Wadanda suke danne hakkin kananan jarumai da crew, kuma su hana su magana. su kuma su kasa magana saboda kar gobe suki kiransu aiki.”

Sakon da ya wallafa a shafin sa

Adam Zango yayi kira ga sauran abokan aikin sa da su rungumi sabuwar akida wanda ya kafa mai take “Tafiyar Gyaran Karaya”

Yace kofa a bude yake ga masu neman hada hannu wajen neman hakkinsu domin a yanzu shi kadai ne a cikinta.

KARANTA: Adam Zango Ya Yi Kira Da Ayi Zanga Zanga Akan Soke Ginin Dandalin Fim

Wannan dai ba shine karo na farko ba da jarumin zai nuna facin ran sa game da abubuwa dake faruwa a masana’ antar kannywood ba. A kwanakin baya ma ya fitar da wata budaddiyar wasika zuwa ga mahassadan shi masu neman bata masa suna a masana’ antar kannywood, ya ce zai saka wando daya da duk wanda ke neman yi masa kazafi

Jarumin ya fitar da fushinsa a shafinsa na kafar sadarwa ta instagram inda ya kira kansa da damisa kuma wanda ya nemi shi da fada ba ya neman zaman lafiya.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...