Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Da Ke AKe: Tsaftar Mace Mai Al’ada

0 1,404

Wasu matan da jinin al’ada ya sauko musu sai su ƙazanta kansu, ba wanka ba kwalliya, su ƙaurace wa miji hatta wasannin soyayya basa yi da shi. Sati ɗaya, sati biyu, kullum haka suke.

 

Ina kwallin idanuwa?

 

Ina jan-baki da gazal?

 

ina hoda ina turare?

 

Inaaaa! duk ta watsar dasu, tir da mai haka don ba tsari bane.

 

Kar ki sake ki faɗa cikin wannan kuskuren, Musulunci bai hana wanka da kwalliya da wasa da miji, dan ana al’ada ba.

 

Manzon Allah S.A.W ya ce, “Kuyi komai ban da saduwa”. Muslim ne ya rawaito.

 

Barin kwalliya da zaman ƙazanta lokacin al’ada, al’adar yahudawa ce.

 

Sune idan mace ta fara jini, sai a ƙaurace mata, ta koma cikin ɗaki ta zama ba fita, kuma ba mai shiga wurinta, abinci ma sai dai a jefa mata har sai ta gama jini.

 

Musulunci ba haka yake ba. Al’ada bata hana hira da miji, ko yin kwalliya, ko rugume juna ko wasannin soyayya, saduwa ce kaɗai aka hana,’yar uwa!

 

#dakeake

 

27-R/Auwal-1439H

15-December-2017M

 

Hadiza Balanti

FOUNDER | CEO

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

BN2399256    TIN19603064

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...