Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Dabi’u 6 Da Ke Hana Ma’aikatan Ofis Aikinsu yadda ya Kamata

0 698

Da dama a kasar Nijeriya ana tashi daga aiki ne da karfe 4 na yamma. Koda yake wasu na kaiwa har karfe 5.

Sai dai ya kamata a matsayinmu na ma’aikata masu burin wata rana muma mu dauki ma’aikata don yi mana aiki a sana’o’in da muka bude, mu san cewa yawan aiki ko kuma cimma manufar aiki na yau da gobe.

A saboda haka n ma ya kamata mu san dalilai ko abubuwan da ke hana ma’aikaci ofis yin aikinsa yadda ya kamata

Dabi’a ta farko:  Dabi’ar nan ta bude kafafen yada zumunta a lokacin aiki ya yi matukar tasiri wajen rage himmar ma’aikata da ma abinda za su iya cimma a kowace rana. Sau tari za ka ga ma’aikata na bude shafin facebook, ko na Instagram, ko na twitter ko snap chat da sauransu. Da zarar wani abu ya daukewa ma’aikaci hankali daga abinda ya ke yi. to fa yana da matukar wahala hankalinsa ya dawo kan aikin 100 bisa 100, wanda hakan dole ya shafi aikinsa da manufar da ya kamata ya cimma a wannan rana

 

 

Dabi’a ta biyu: Rashin karin kumallo – Wasu ma’aikata sun mayar da ita dabi’arsu yin karin kumallo a makare. Wasu ma sam ba sa yin karin kumallon. Hakika wannan hali na shafar aiki, domin sau tari za ka ga ma’aikaci na fama wajen kammala wani dan aiki da ya kamata ya kammala cikin sauki, amma saboda yunwa da ke damunsa, aikin ya zame masa babban aikin da sai a bata lokacin da bai kamata irin wannan aikin ba

 

 

Dabi’a ta uku: Zama Waje Daya: Ba daidai bane ma’aikacin ofis ya zauna a kujerarsa ya ki motsawa. Wannan ko shakka babu yana haifar da cushewar kwakwalwa, ciwon baya da gundiri sakamakon dadewa a waje daya. Da zarar ma’aikaci ya samu daya daga cikin wadannan abubuwa da lissafa ko duka, to fa dole manufar da ake so a cimma a aikin zai yi kasa

 

Dabi’a ta hudu: Sanya Earphone (abinda ake sanyawa a kunne don sauraren kida) – Wasu ma’aikata na ganin cewa yin amfani da na’urar earphone a lokacin da suke aiki na taimaka musu wajen rage samuwar abubuwan da za su dauke musu hankali, to, amma, shi kanshi aiki da kuma sauraro a lokaci guda na haifar da rashin natsuwa da samuwar dauke hankali

 

 

Dabi’a ta Biyar: Makara– Makara na daga cikin manyan dalilin da ke hana ma’aikaci gabatar da aikinsa yadda ya kamata. Bincike ya nuna cewa makara zuwa wajen aiki ya haifar da rashin cimma manufa na yau da gobe ga kamfaninnika a fadin duniya, wannan ne ma ya sanya kamfaninnika ba sa yarda da dabi’ar makara daga ma’aikatansu. Da zarar ma’aikaci ya makara, komai nasa zai rushe domin zai rasa nutsuwa, hakan kuma zai shafi yadda zai kama aiki da yadda  zai dire a ranar

 

Dabi’a ta Shida: Hira da abokan aiki – Doguwar hira da za ta saka a bar aiki, musu da jayayya akan wani batu wanda bai shafi aiki ba ko shakka babu yana shafar yadda aikin ma’aikaci zai tafi a wannan ranar. Tsunduma cikin hira na kawo bata lokacin da ya kamata a yi amfani da shi wajen cimma wata manufa kuma a lokuta da dama hira kan kashe wa ma’aikaci karsashin aiki, ta yadda ko bayan ya gama hirar sai ya gagara komawa kan aiki ka’in da na’in

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...