Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Daliban Makarantar Sakandire 5 Sun Nitse a Kogin Kaduna

0 510

Daliban wata makarantar sakandire a Kaduna sun gamu da ajalinsu bayan da suka nitse a kogin Kaduna yayin da suka je yawon bude ido.

Kimani daliban makarantar guda 73 suka tafi yawon bude idon a hukumar samar da ruwa ta jahar, tare da malaman su biyu da misalin karfe 11:00 na safiyar jiya Laraba.

Daliban da suka rasa rayukan su ‘yan aji biyar ne, maza hudu da mace daya. Sun hada da: Priscilla Romania, Goodness Aromilade, Monday Umahi, Joseph Benedict da David Ukegbu, masu shekaru tsakanin 14 da 16.

KARANTA WANNAN: Mutane na sayar da yara kamar gyada a jahar Kaduna – Haj. Hafsat

DPO na ofishin ‘yan sanda da ke yankin Kakuri, CSP Benshak W. Dakyer ya fadawa manema labarai cewa da farko yara 10 ne suka nitse, amma an samu nasarar ceto 5 da ransu.

Daya daga cikin yaran da aka ceto ya fadawa manema labarai cewa ya tsallake rijiya da baya ne bayan da ya rike karfen da ke gefen kwale kwalen a lokacin da ya yi hatsari, daga nan sai ya yi iyo ya fito daga ruwan.

Ya ce “Abokai na ma sun yi kokarin fitowa daga ruwan, amma karfin ruwan ya yi yawa, shi ya sa suka kasa”

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...