Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Kori Malaman Firamare 25,000 Na Kano Da Basu Da Ƙwarewar Aiki Ba- Ganduje

0 1,608

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, a jiya Alhamis ya bayyana dalilin da ya sa ba zai sallami malaman firamaren makaratun gwamnatin jihar kimanin 25,000 da basu da cancanta sakamakon rashin ƙwarewar aiki da basu da ita daga aikinsu ba

 

Gwamnan ya faɗi hakan ne a fadar gwamnatin jihar a yayin da ya ke miƙa abubuwan tallafi ga matasa 550 da kuma bashin kudin sayen mota ga ma’aikatan jihar 2,600

Buɗe Ka Karanta: An Kama Mutanen Da Suka Sayar Da Yaro Dan Shekara 5 Akan N15,000

Gaduje ya ce “Gwamnatina ta gaji malaman firamaren da basu da ƙwarewa aƙalla 25,000, amma a maimakon mu koresu daga aiki, mun ɗauki matakin mayar da su makarantu don samun horo na matakin karatun NCE. Mun yi hakane saboda imani da muka yi cewa sallamrsu daga aiki ba zai haifawa jihar nan tamu ɗa mai ido ba saboda talauci da rashin aikin da korar tasu zata haifar”

 

Ganduje ya ci gaba da cewa, “Gwamnatina a shirye ta ke da ta tabbatar da tafiyar ayyuka daidai wa daida ta hanyar samar da ma’aikata ƙwararru kuma waɗanda suka cancanta a kowane mataki da rukuni don su yi wa jihar Kano aikin da zai raya jihar”

 

“Mun kuma samar da tsarin bayar da bashi ga ma’aikata don mu ƙwarara gwiwoyinsu tare kuma da cire tinja-tinjar da ke tsakanin darajar aikin da ake baiwa masu kwalin digiri da masu HND”

Karanta Wannan Ma: EFCC Ta Gano Maƙudan Kuɗaɗe A Asusun Ajiyar Uwar Patience Jonathan

Daga ƙarshe, Ganduje ya ja hankalin matasa 550 da suka yi nasarar samun tallafin gwamnatin  da su guji yin amfani da tallafin wajen aiwatar da abubuwan da suka ci karo da dalilan da ya sa gwamnati ta miƙa musu tallafin

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...