Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Dalilin Da Ya Sa Buhari Ke Goyon Bayan El-Rufa’i Game Da Korar Malamai – Shehu Sani

0 206

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce rashin sani ne ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke goyon bayan aniyar gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufa’i na korar malaman makaranta kimanin 21,780.

Idan mai karatu bai manta ba, a watan Nuwambar 2017 ne shugaban kasa Buhari ya fito fili ya goyi da bayan El-Rufa’i game da wannan batu.

El-Rufa’i ya ce sauye sauye a bangaren ilimin jahar zai tabbatar da ingancin ilimi tare da alkawarin zai dauki sabbin kwararrun malamai guda 25,000 idan abun ya tabbata.

KARANTA WANNAN: An sace babban mataimakin Sanata Shehu Sani

Sai dai sanatan sam bai gamsu da wannan batu ba. Shehu Sani ya ce lamarin ba komai bane illa kama karya da zaluntar ma’aikatan jahar.

Ya ce hasali ma korar malaman bai halarta ba.

Ya kuma yi Allah wadai da yunkurin gwamnatin na hana ma’aikatan fita zanga zangar kalubalantar wannan batu.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...