Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Dan sanda Ya Kashe Dalibar Kwaleji Kan Cin Hancin N200

0 162

Rahotanni sun bayyana cewa wani jami’in dan sanda mai suna Sajan Abua ya harbe wata dalibar kwalejin kimiyya da fasaha mai suna Sofia Oghogho har lahira a garin Igbuzo dake jihar Delta,

Tare da wadanda dan sandan ya harba akwai  ma’aikacin gwamnati mai suna Victor Emeagwai a wani shingen tsaro na binciken motoci masu wucewa a garin Igbuzo.

Lamarin ya faru ne bayan da Sofia da Emeagwai da kuma wani abokinsu Jerry Akinlabi wanda shine direban motar suka zo wucewa a motarsu kirar Toyota Corolla a hanyar Igbuzo.

Isowarsu shingen yansandan dake kusa da kasuwar Igbuzo ne wani dansanda ya bukaci direban ‘Akinlabi’ ya bashi cin hancin N200, shi kuma direban ya hana shi tare da zurawa da gudu. Hakan ya harzuka ‘yansandan suka budewa motar wuta tare da yin harbi inda harbin ya samu sofia da Emeagwai.

Sofia dai ta mutu bayan an garzaya da ita asibiti kuma tuni rundunar ‘yansandan jihar suka kama ‘yansanda guda uku dake aiki a shingen tare da shugabansu ASP Akhabue bayan da Akinlabi ya kai kara zuwa ga kwamishinan ‘yansandan jihar.

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...