Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Dubban Jama’a Sun Sauya Sheka Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC A Kwara

Dubban Jama'a Sun Sauya Sheka Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

0 152

Dubban jama’a magoya bayan jam’iyyar PDP na Agbonda da ke gudunar Ajase II a karkashin karamin hukumar Irepodun a jihar Kwara sun sauye sheka daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC.

 

Karanta wannan: Wani Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2019

 

Mutanen da suka sauye shekar sun bayyana dalilin da ya sa suka sauye sheka daga jam’iyyar inda suka ce jam’iyyar ta yashe su.

 

Karanta wannan: Za Mu Baiwa Buhari Kuri’u Miliyan 5 Idan Ya Tsaya Takara a 2019 – Ganduje

 

Sakataren jam’iyyar APC na jihar, Mr. Olabode Adekanye, ya karbi jama’ar da suka sauye shekara a madadin jam’iyyar a yayin da ake gudunar da wani shirin tallafi da ya shiryawa jama’ar Ajase mai taken =: ‘ABS Ajase II Empowerment Scheme’.

 

Abubuwan da aka raba sun hada da kekunan dinki, injunan nika da kuma fankoki.

 

Karanta wannan: Miji Ya Kashe Matarshi Kuma Uwar ‘Ya’yanshi Guda 5 da Adda

 

Adekanye ya ce sauye shekar da magoya bayan jam’iyyar PDP suka yi lallai ya nuna cewa gwamnatin jihar a karkashin jagorancin jam’iyyar APC ta cimma kudirorin al’ummar jihar da suka zabe ta a lokacin zabe.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...