Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

EFCC Ta Gano Makudan Kudade A Asusun Mahaifiyar Patience

0 612

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta bayyana gano makudan kudade har naira biliyan 2.11 a asusun ajiyar wasu kamfanoni mallakar uwargidan tsohon shugaban kasar Nijeriya Patience Jonathan da Mahaifiyarta marigayiya Mama charity Oba.

Rahoton ya nuna cewa Patience Jonathan ta yi amfani da kungiyoyi masu zaman kansu wajen tabka almundahana  inda hukumar EFCC ta ce ta gano akalla naira biliyan 17 da hukumomi gwamnati suka biya cikin asusun ajiyar kamfanonin Patience a lokacin mulkin Goodluck.

Hukumar ta kayyade kudade da suka shiga asusun ajiyar a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2015 wanda mafi yawan  kamfanonin na dauke ne da sunanyen ‘yan aikinta na cikin gida.

Rahoton ya kuma ce, Hukumar EFCC ta gano wasu kudade miliyan 200 na kwangila da hukumar NITDA ta biya cikin asusun mallakar kamfanin mahaifiyar Patience mai suna “Magel Resort” wanda a yanzu haka hukumar na cigaba da bincike a kai.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...