Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Etisalat Na Dab Da Durkushewa

484

Kamfanin sadarwa ta wayar hannu ta Etisalat Nijeriya na dab da tattara ya nasu-ya nasu su bar Nijeriya bayan da babban kamfanin nan na kasar United Arab Emirates da ya sanya hannun jari a kamfanin wato Mubadala Development Company suka janye jarin da suka saka kuma suka fice suka bar kasar Nijeriya

 

Kamfanin Mubadala, majiyarmu ta bayyana cewa shi ke da kaso 70 cikin 100 na jarin Etisalat inda EMTS da Bello Osagie ke jagoranta ke mallakar ragowar kaso 30 din da ya rage

 

Tuni dai dama Mubadala ta sanar da Etisalat Nijeriya da hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasar Nijeriya NCC bukatarta na ficewa daga Nijeriya

 

Kamfanin Etisalat Nijeriya dai a baya-bayan nan ya fada matsalar tabarbarewar tattalin arziki tun lokacin da bankuna a ciki da wajen Nijeriya a karkashin jagoranci Zenith Bank suka matsa wa kamfanin ya biya bashin da ake binsa da ya kai dalar Amurka biliyan 1.72 daidai da Naira biliyan 541.8 da kamfanin Etisalat ya ci a shekarar 2015

 

Etisalat ta ciwo bashin ne don ta inganta harkokin gudanarwarta da karfafa layinta a fadin Nijeriya

 

Gaza cika alkawarinta na biyan bashin a shekarar 2016 ya sanya bankunan da suka bata bashin a ciki da wajen Nijeriya suka hada kai a karkashin jagorancin Zenith Bank suka yi karar Etisalat ga Babban Bankin Nijeriya CBN da kuma Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Nijeriya NCC

 

NCC ta sanya baki wajen shiga tsakanin bankunan da Etisalat Nijeriya wajen ganin cewa bankunan ba su karbe ikon Etisalat din ba. Inda aka sake zama a teburin sulhu aka fitar da sabon lokacin Etisalat za ta biya bashin

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...