Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

An Gano Kan Wani Dan Sanda Da Aka Kashe A Dakin Asiri

0 1,003

An gano kan sifeton ‘yan sanda wanda aka kashe a ranar bikin Kirisimeti a wani dakin asirin gargajiya.

 

Kwamishinan ‘yan sanda reshen na reshen jihar Ribas, Hafiz Mohammed, ya gabatar da matsafan da suka kashe sifeton ‘yan sanda tare da wasu mutane ne 529 wadanda ake zargi da aika laifuka daban daban a lokacin bikin kirisimeti.

 

Karanta wannan: Wasu Matsafa 2 Sun Yi Gunduwa Gundunwa Da Wata ‘Yar Shekaru 17 Mai Tallar Gugguru

A yayin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Calabar a jiya, kwamishina Hafiz, ya ce wadanda aka gabatar sun aikata laifuka da daban daban wadanda suka hada da kisan kai, da fashi da makami, da lalata kayayyakin gwamnati, sace mutane tare da yiwa kananan fyade.

 

Karanta wannan: ‘Yan Sanda A Jihar Kwara Na Sayar Da Mutanen Da Suka Daɗe A Komarsu A Tsare Ga Matsafa AKan Naira Dubu 80

 

Inuwa ya bayyana cewa sifeton da aka kashe ” a 25 ga Disamba 2107, Sifeto Micheal Umoh, ya kasance yana aiki a sashen yaki da fashi da makami na ‘yan sanda na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Enugu a yayin da ya ziyarci surukkansa da ke kauyen Ojor tare da iyalansa.

 

Karanta wannan: Wata Dalibar Makaranta Ta Kubuta Daga Hannun Matsafa

 

An kashe sifeto Micheal ne a yayin da ya fita neman man fetur a motsarsa inda matasan kauyen Uyangha wanda ke karkashin karamar hukuamr Akamkpa suka kai masa hare suka yana hare, suka yanke kansa sannan kuma suka kai kan na sa zuwa wani dakin asiri da da ke kauyen Uyangha.

 

Karanta wannan: Wasu Asibitoci Na Siyarwa Matsafa Sassan Mutane – Inji ‘Yan Sanda

 

Matasan da suka kashe shi sun dauke Bindigan AK-47 wanda ke hannun sa sannan kuma suka cinnawa motarsa kirar Sienna wuta. Har yanzu ba a san inda gangar jikinsa ya ke ba amma a gano kan sa a wani dakin asiri da ke kauyen.

 

Ya ce bincike ya sa an cafke Ophot Valentine Ebani, 54 years, ( shugaban gargajiyan kauyen Uyangha), da Isaac James Akpan, da Benjamin Phiilp, da Patrick Effiong, da Famous Mfon, da Effiong Peter, da Ndifon Arong, da kuma Wisdom Bassey Inok.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...