Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gargadi: Rashin Yafiya Na Haifar Da Cutar Daji Mai Naci – Masana

0 294

Wani bincike da aka gudanar a kwana kwanan nan a kasar Amurka na nuna cewa akalla kaso 59 zuwa 61 na cutar daji mai naci na da alaka da rashin yafiya.

Wani masanin mai suna Dakta Patrick Ijewere wanda ma’aikaci ne a Jami’ar Howard da ke Washinton DC a kasar Amurka shi ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN a yayin da ya halarci taron kayan shaye shaye na duniya da aka gudanar a jahar Lagos.

Dakta Ijewere ya ce akwai binciken kimiyya da dama da suka nuna alaka tsakanin halayyar mutane da cututtukan da ka iya kama su.

A cewar shi “Bincike ya nuna cewa akalla kaso 61 na maza da 59 na matan da ke fama da cutar dajin da ya ki jin magani su na da matsalar rashin yafiya”

KARANTA WANNAN: Gargadi daga masana: Shan Shisha na haddasa cutar dajin Huhu

“Wannan ba wani abu bane mai wahalar fahimta. Akai wani sinadari a jikin dan adam mai suna Cortisol. Wannan sinadari wanda ke hana garkuwar jikin mu aiki ya na da alaka da fushi”

Wani masanin daban mai suna Dakta Steven Standiford ya bayyana rashin yafiya a matsayin cuta mai zaman kanta saboda ya na sanyawa mutane cuta ya kuma dawwamar da su a cikin ta.

A cewar shi , “A cikin gaba daya mutanen da ke fama da cutar daji, kaso 61 na fama da rashin yafiya, kuma kaso 50 daga cikin su lamarin ya wuce gona da iri”, ya fadawa NAN.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...