Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gasar Cin Kanbin Namiji Mafi Muni: Kalli Hotunan Munanan Mazan Da Suka Shiga Gasar

0 981

Gasar cin kanbin mace mafi kyau “Miss Beauty” da namiji mafi kyawu “Mr. Macho” wata gasa ce da ta samu gindin zama a matakan kananan hukumomi a wasu bangarorin duniya, a matakin jihohi, a matakin kasashe da ma a matakin duniya baki daya. Kai makarantu da dama ma na yin irin wannan gasar a matakin aji-aji da dai sauransu

 

Sai dai ba kasafai aka faye jin gasar mafi muni ba, in banda a ‘yan shekarunnan da ake kokarin su ma munana a tafi da su. Ma’ana su ma kar a bar su a baya wajen shiga gasa da karbar kanbi da kyaututtuka, tunda dai Allahn da ya yi mai kyau, shi ne ya yi mummuna

 

A kasar Zimbabwe, William Masvinu, mai shekaru 43 ya sake lashe kanbin namiji mafi muni a karo na hudu a bayan da ya doke abokan karawarsa

Masvinu, wanda ya fito daga yankin Epworth ya yi rashin nasara a bara, amma a daren Lahadin da ta gabata, ya sake dawo da kanbinsa bayan ya samu maki 98 a gasar da aka gudanar a babban birnin Zimbabwe, Harare

Masvinu ya samu kyautar dalar Amurka 500 da kuma kosasshen sa guda daya, sai mai bi masa, Fanuel Musekiwa ya samu kyautar dalar Amurka 200, inda wanda ya zo na uku, Maison Sere ya samu kyautar dalar Amurka 100

A bayaninsa na bayan taro, Masvinu ya ce “Babu tantama babu wanda ya kai ni bare har ya fi ni muni a fadin kasar Zimbabwe”

“Ko shakka babu gasar ta yi matukar tsanani sakamakon dukkanmu wadanda muka shiga gasar munana ne kuma kowannenmu zai iya samun nasara. Amma daga karshe na samu nasara, inda hakan ya dada tabbatar da matsayina na sarkin munin Zimbabwe. Ina godiya ga Ubangijina kuma mai alfahari da muni na”

“Burina shi ne na in samu nasarar cin wannan gasa a matakin duniya in har ana yin gasar a matakin duniya,” inji Masvinu

Shi kuwa Musekiwa cewa ya yi, zai kara himma a gasar badi don ganin ya doke mai rike da kanbin

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...