Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gobara Ta Kashe Miji Da Mata Mai Dauke Da Juna Biyu Tare Da Yaransu 2

0 73

Gobara ta kama da wasu ma’aurata tare da ‘ya’yan su 2 a gida mai lamba 13, da ke unguwar Bariga a birnin Legas.

 

Karanta wannan: Gobara Ta Cinye Dakunan Dalibai Mata A Makarantan Sakandaren F.G.C Keffi

 

An samu labarin cewa ma’auratan ke da wani kantin magani wanda ke hade da gidan inda gobarar ya kama.

 

Karanta wannan: Dangote Ya Tallafawa ‘Yan Kasuwar Kano Da Gobara Ta Lakume Kayan Su Da Naira Miliyan 500

Gobara ya kama a misalin karfe 2:00 dare a ranar Laraba.

 

Har yanzu dai ba a san abunda ya tada gobarar ba. Makwabtan su sun bayyanawa manema labarai da cewa wata kila karfin wutan lantarki ne ya jawo gobarar, a yayin da wasu daga cikin suka ce wata kila sun kunna kyandir a bisa kan wani katako bacci ya dauke su suka  manta da shi.

 

Karanta wannan: Gobara Ta Lankwame Gidan Karamin Ministan Mai ‘Ibe Kachikwu’

 

Ma’auratan tare da ‘ya’yan su sun yi bacci a yayin kyandir din ya ida ci har ya fara cin tebur din da suka aza kyandir din a kai. Daga baya har ya kai ga kama da kayayyakin sawa da aka aje a kusa da teburin

 

Karanta wannan: Fisabilillah: Wani Bawan Allah Da Ya Gamu Da Hatsarin Gobara Na Neman Taimakon ‘Yan Uwa Musulmi

 

Jami’an hukumar kashe  gobara ta jihar Legas, da na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas tare da kuma jami’an tsaro na ‘yan sanda na yankin wadanda ke daga ofishin ‘yan sanda na yankin Bariga sun amsa kirar neman agajin da mazauna yankin suka yi masu, amma kafin su isa gidan da gobarar ta kama iyalan sun kone.

 

Karanta wannan: Gobara Ta Kashe Mutane 4 A Tudun Murtala A Jihar Kano

 

Wani mai zama a kusa da gidan da gobarar ya kama,  Kayode Ibrahim, ya ce wutan ya riga ya bazu a bangarori daban daban na gidan kafin makwabtan na su suka san da gobarar sannan suka neme agaji. A cewarsa, gobarar ya ci waus shaguna 2 na makwabtan mamatan.

 

Karanta wannan: Za a Gurfanar Da ‘Yan Kungiyar IPOB Guda 59 a Kotu Akan Laifukan Kisa Da Tada Gobara

 

“Hayakin wutan ya halaka ‘ya’ya ma’auratan 2 kafin wuta ya samu zuwa gare su. Abun ya razana mutane dayawa,” ya ce.

 

Karanta wannan: Wani Mutum Ya Babbaka Kan Shi Da Wuta Bayan Ya Kashe Matar Shi

 

Daraktan hukumar kashe gobara na jihar Legas, Razaq Fadipe, ya ce an tsince gawarwakin wadanda gobarar ya kama da su a cikin wani shago 1 daga cikin shaguna 3 da gobarar ya ci.

 

Karanta wannan: Uwa Ta Shake Jaririnta Dan Wata 8 Da Wayar Wuta

 

Fadipe ya tabbatarwa manema labarai da cewa iyalan na zama a cikin daya daga cikin shagon ne, wanda ya kasance kuma shagon kantin maganin su ne.

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...