Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa

0 340

 

Manchester United na son daukar dan wasan baya na Tottenham Danny Rose mai shekaru 27 in an bude tagar saye da sayar da ‘yan wasa a watan Janeru

 

Manchester City na neman Faouzi Ghoulam na Napoli domin ya cike gurbin da Benjamin Mendy ya bari bayan da ya yi rauni

 

Barcelon za ta gaggauta biyan kudin da aka saka don daukar dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antoine Griezmann na fam miliyan 89 kafin a kara farashin a karshen kaka mai zuwa

 

PSG na kokarin sayar da dan wasanta na gefe, Angel di Maria ga wata kungiya a kasar China a watan Janeru mai zuwa

 

Arsenal ta kulla yarjejeniya da tsohon dan wasanta Marc Overmars mai shekaru 44 don ya bar kungiyar Ajax ya zo ya zame mata daraktan kwallon kafa na kungiyar a kaka mai zuwa

 

Andrea Pirlo ya karyata batun cewa zai dawo Chelsea a matsayin daya daga cikin masu horar da ‘yan wasa a karkashin koci Conte da zarar ya yi ritaya daga buga kwallo a karshen kakar bana

 

Hasashe na nuna cewa, Antonio Conte zai koma kasarsa ta Italiya a matsayin mai horar da tawagar kasar bayan da kasar ta kai ga samun damar buga wasan da zai bata nasara shiga gasar cin kofin duniya da kyar a karkashin koci Gian Piero Ventura

 

Kocin Manchester United na cikin wadanda suka kalli wasan da aka kara tsakanin Austria da Serbia da nufin kallon yadda dan wasan da ya ke marari, Mijat Gacinovic mai shekaru 22

 

Kungiyar Crystal Palace ta aika da tawagarta don duba yadda dan wasan gaba na Besiktas, Cenk Tosun zai taka leda a karawar Turkey da Iceland a ranar Juma’a

 

Brigton za ta dauke dan wasan gaba na Newcastle, Aleksandar Mitrovic mai shekaru 23 a watan Janeru mai zuwa

 

 

Kungiyar Galatasaray na neman dan wasan baya na Manchester United, Daley Blind

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...