Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa…

0 577

 

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Oscar Grau ya ce kungiyar za ta sake shiga zawarcin Philippe Coutinho a watan Janeru mai zuwa da nufin dauke shi daga Liverpool

 

 

Mundo Deportivo ta rawaito ta kafar Daily Mail cewa Liverpool ta amince Coutinho ya koma Barcelona a watan Janeru in har Barca za ta biya fam miliyan 98.6

 

 

Jose Mourinho ya shirya tsaf don sanya hannu a takardar sabunta kwantiraginsa da Manchester United. Sabuwar yarjeniyar ta kunshi kwangilar aiki na shekara 5 akan fam miliyan 65

 

 

Juan Mata na Manchester United ya ki karbar tayin da wata kungiya a kasar China ta yi masa na ya dawo gidanta da murza leda

 

 

Jack Wilshere na Arsenal ya damu matuka na da ya bar Arsenal a watan Janeru mai zuwa don ko ya samu gurbi a tawagar Ingila da Gareth Southgate ke jagoranta zuwa cin gasar kofin duniya

 

 

Dan wasan baya na PSG, Dani Alves ya ce zai yi matukar dacewa in har PSG ta sayi Alexis Sanchez daga Arsenal in kwantiraginsa ya kare a karshen kakar bana

 

 

Wakilin dan wasan tsakiya na Arsenal, Mesut Ozil ya ce tattauna sabunta kwantiragin dan wasan a Arsenal na tafiya yadda ya kamata

 

 

Kocin Crystal Palace, Roy Hodgson na shirye-shiryen sayen kwararrun ‘yan wasa a watan Janeru a wani yanayi na fitar da kungiyar daga jerin kungiyoyin da suke ajin ralageshin

 

 

 

Chelsea na cikin fargabar watakila raunin N’Golo Kante ba zai barshi ya buga dukkan wasanni 6 da kungiyar za ta buga a wannan wata na Oktoba ba

 

 

Arsenal za ta kara da Liverpool da misalin karfe 1:30 na ana gobe Kirismeti

 

 

Kungiyoyin Burley, Newcastle United da West Brom na son daukar dan wasan baya na Inter Milan Yuto Nagatomo mai shekaru 31

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...