Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa… FA Za Ta Hukunta Pogba

0 898

Akwai yiwuwar tsawaita dakatarwar da za a yi wa Paul Pogba amatsayin hukunci bisa tafi da ya yi wa alkalin wasa bayan ya daga masa jan kati a wasan da Manchester United ta kara da Arsenal a ranar Asabar din da ta gabata

 

 

Kocin Everton, Sam Allardyce ya bayyana dan wasan gaba na Watford, Troy Deeney mai shekaru 29 a matsayin bukatar Everton na farko a watan Janeru mai kamawa

 

 

 

Sam Allardyce ya bayyana bukatarsa na son kar Ross Barkley ya tafi, amma ya ce in har burin Barkley shi ne na ya bar Everton, to zai iya yin hakan a watan Janeru

 

 

 

Arsenal na mararin daukar dan wasan tsakiya na Sevella, Steven N’Zonzi mai shekaru 28, bayan da dan wasan ya samu matsala da kocin Sevilla, Eduardo Berizzo

 

 

 

Arsenal za ta kara da Tottenham wajen fafutukar daukar Dani Ceballos wanda aka ce baya farin ciki da zamansa a Real Madrid saboda rashin bashi dama da ba a yi

 

 

 

Dan wasan tsakiya na Schalke, Leon Goretzka mai shekaru 22, zai bayyanawa kungiyoyin Manchester United, Barcelona da Arsenal tsare-tsarensa a watan Janeru mai kamawa sakamakon nemansa da kungiyoyin uku ke yi

 

 

 

Tottenham na shirin aikawa da Yusuf Yazici goron gayyata don ya dawo kungiyar da taka leda. Yazici mai shekaru 20 dai yana bugawa kungiyar Trabzonspor ta kasar Turkiya ne a halin yanzu

 

 

 

Kungiyar Gremio ta kasar Barazil ta fadawa Barcelona cewa, in har tana son ta dauki dan wasanta na tsakiya, Arthur mai shekaru 21, to fa sai ta ajiye fam miliyan 44

 

 

 

Mataimakin kocin tawagar kasar Faransa ya bayyana cewa, in har Olivier Giroud na son ya wakilci a kasar a gasar cin kofin duniya a badi, to fa sai in kungiyarsa ta kara masa adadin lokacin da ta ke ba shi na damar buga wasanni ko kuma Giroud din ya sauya sheka

 

 

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya ja hankalin hukumar gudanarwar kungiyar da ta tabbata ta sabunta kwantiragin mai tsaron gida, Thibaut Courtois da dan wasan tsakiya, Eden Hazard kafin lokacin da za a tafi hutun cin kofin duniya

 

 

 

‘Yan wasan tawagar kwallon kafa ta Ingila za su raba fam miliyan 5 a matsayin tukuici in har sun yi nasarar daga kofin duniya, amma in har aka cire su daga matakin rukuni, to babu abinda kasar za ta basu

 

 

 

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bayyana cewa ba za kori kocin tawagar, Southgate, ba ko da kuwa tawagar ta kasa tabuka abin arziki a gasar cin kofin zakarun turai

 

 

Tottenham ta tabbatarwa da Manchester United cewa a shirye ta ke da ta sayar mata da Danny Rose in har ta ajiye mata fam miliyan 45

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...