Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa… Real Madrid ta so ta yi wa Barca shigar sauri akan batun sayen Coutinho

0 820

 

Dan wasan gaba na Faransa da Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya ce a shirye yake ya share zuwa Barcelona in har Manchester United za ta biya albashin fam dubu 400 a kowane mako

 

Barcelona ta sayi Coutinho akan farashin fam miliyan 142 daga Liverpool kuma za a gabatar da Coutinho ga magoya bayan kungiyar a yau Litinin

 

Za a dan jinkirta fara sanya Coutinho a wasanni a matsayinsa na dan wasan Barcelona sakamakon dan karamin rauni da ya zo da shi

 

Liverpool ta shiga neman Thomas Lemar daga Monaco a matsayin dan wasan da zai cike gibin da Coutinho ya bari

 

Na gaba-gaba a ‘yan wasan da Real Madrid za ta nema a karshen kakar bana shi ne Eden Hazard na Chelsea, sai kuma mai tsaron gidan Chelsea din, Thibaut Courtois

 

Real Madrid ta so mikawa Liverpool fam miliyan 177 don dauke Philippe Coutinho kafin ya kulla yarjejeniyar kwantiragin fam miliyan 142 da Barca inda har sai da ya cikawa Liverpool fam miliyan 11.5 daga kudin

 

Dan wasan tsakiya na Shakhtar Donetsk, Fred mai shekaru 24 da haihuwa ya ce kawai jiran kiran kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ke yi

 

Newcastle na fatan kammala sayen dan wasan gefe na Chelsea, Kennedy mai shekaru 21

Karanta Wannan: Real Madrid Za Ta Mikawa Tottenham Kudi Da Bale Don Daukar Kane

Leicester City ta kusa kammala daukar dan wasa na farko da za ta saya a wannan tagar ta Janairu, inda ciniki ya yi nisa na sayen dan wasan gaba na Gazelec Ajaccio, Fousseni Diabete akan fam miliyan 1.7

 

Dan wasan tsere, Usain Bolt ya bayyana cewa yana atisaye da kungiyar Borussia Dortmund, amma a zuciyarsa ya fi so ya bugawa Manchester United

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...