Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa… Rikitic Na Son Barin Barca Sakamakon Zuwa Coutinho

0 369

 

Manchester ta shirya tsaf don sake mika sabon tayi ga Arsenal don daukar Alexis Sanchez tare kuma da fatan Arsenal za ta amince ta sallama mayta dan wasan a wannan watan

 

Sanchez zai ki karbar tayin karin albashi da adadinsa ya kai fam miliyan 25 a shekara don ya koma Manchester City a wannan wata na Janairu

 

Arsenal ta ce a shirye ta ke da ta bar Sanchez ya sauya sheka matukar za a mika mata fam miliyan 30 ko wani abu kusa da haka, kuma in har za a cinikin da wuri ta yadda za ta samu damar sayen madadinsa kafin a rufe tahar saye da sayarwar na wannan wata

 

Wata majiya kusa da Sanchez ta bayyana cewa dan wasan zai iya komawa Manchester City a wannan makon

 

Arsenal ta bayyana dan wasan Monaco, Thomas Lemar a matsayin magajin Alexis Sanchez

 

Arsenal da Liverpool na mararin Ivan Rikitic na Barcelona bayan da dan wasan ya bayyana ra’ayinsa na son barin Barca sakamakon zuwa Philippe Coutinho

Karanta: FA Za Ta Hukunta Pogba

Dan wasan tsakiya na Arsenal, Francis Coquelin zai bar Arsenal a watan nan na Janairu sakamakon sansana da ya ke samu daga kungiyoyin West Ham da Valencia

 

Chelsea ta janye daga son daukar Alex Sandro ne sakamakon kudi da ta ce Juventus ta tsulawa dan wasan da ya kai fam miliyan 60

 

Harry Kane ya bayyana cewa baya cikin wata damuwa kasancewarsa a Tottenham, kawai dai da akwai bukatar kungiyar ta fara daga kofuna

 

Leicester za ta bar Kelechi Iheanacho na Nijeriya ya bar kungiyar a watan nan duk kuwa da cewa bata fi watannin biyar da sayensa ba akan fam miliyan 25

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...