Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa… Zidane da Florentino Perez Sun Kira Hazard a Waya

0 756

 

Shugaban hukumar gudanarwar Real Madrid, Florentino Perez, tare da kocin kungiyar, Zinadine Zidane, sun kira Eden Hazard na Chelsea a waya don fara tattaunawa da shi don jan ra’ayinsa zuwa Madrid

 

Dan wasan baya na West Brom, Jonny Evans mai shekaru 29 ya zama abin bida daga kungiyoyin Everton da West Ham a yayin da Manchester City ke ci gaba da bayyana sha’awarsu ta daukar dan wasan

 

Machester United za ta yi kakara da Inter Milan, a inda Juan Mata zai koma Inter Milan, shi kuma Joao Mario zai dawo Man Utd in har bangarorin biyun sun aminta da kunshin yarjejeniyar

 

Kungiyoyin Manchester City da Liverpool na wasoson daukar dan wasan tsakiya na Nice, Jean Seri, wanda Barcelona ke kwalamar dauka

 

Leo Messi ya shawarci Javier Mascherano da ya bar kungiyar Barcelona zuwa wata kungiyar da zai samu damar buga wasanni a kai-a kai

 

 

Sai da Leo Messi ya yi burus da albashin fam dubu 850 a mako da Manchester City ta kwadaita masa kafin ya sabunta kwantiraginsa da Barcelona. Cikin abinda Manchester City ta kwadaitawa Messi har da fam miliyan 88 a matsayin garabasar amincewa da komawa Man City

 

Kocin Liverpool ya bayyana cewa ba shi tabbacin Philippe Coutinho zai ci gaba da kasancewa da kungiyar Liverpool daga watan Janeru sakamakon bude wutar da Barcelona ta yi wajen ganin sai ta dauke dan wasan

 

Kocin Manchester City, Pep Guardiola zai sake mikawa Arsenal tayin dauke dan wasan gaba na Arsenal dina watan Janeru, Alexis Sanchez mai shekaru 28

 

Everton ta tuntubi Arsenal kan batun daukar dan wasanta, Theo Walcott

 

Chelsea ta samu daddadan labarin cewa Alex Sandro ya fadawa kungiyarsa Juventus cewa yana so ya bar kungiyar

 

Kocin West Ham, David Moyes na duba yiwuwar ajiye mai tsaron gidan kungiyar, Joe Hart a benci a haduwarsu da Chelsea a ranar Asabar mai zuwa

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...