Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gulma Daga Duniyar Nollywood… Mawakin Rap M.I Abaga Na Tare Da Mutanen Da Ba Za Su Fada Masa Gaskiya Ba – Osagie Alange (Bidiyo)

0 907

Shahararren mawakin rap na Nijeriya wanda aka fi sani da suna M.I Abaga wato Mr. Incredible a cikin ‘yan kwanakin da da suka gabatar ya tafi shafin sa a twitter inda ya soki wani dan jaridan kafafen yada labarai na Pulse mai suna Ayomide Tayo bayan dan jarindan ya ruburu game da yanayin harkar aikin sa na raira wakar rap

 

Akan lamarin, mawaki M.I Abaga tare da mai taimakin shugaban kamfanin shirya wakoki na Chocolate City mai suna Loose Kaynon, suka tafi zuwa ofishin Pulse don su yi magana da dan jaridan Osagie Alonge tare da ‘yan uwan sa ‘yan jarida a shirin Loose Talk.

 

A yayin da suke nazari game da album na M.I Abaga, Osagie ya fadawa M.I Abaga cewa album na sa bai yi ba, inda ya bayyana cewa yawanci yanzu mawaka na siyan ‘yan kallo ne a shafin Youtube sannan kuma “yana tare da mutane ne wadanda ba su iya fada masa gaskiya”.

Ku kalli bidiyon a kasa, a harshen turanci:

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...