Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Guzirin Juma’a: Sadaka Da Yawan Kyauta Ba Sa Karar Da Dukiya – Sheikh Aliyu

0 299

Allah ya yi dan Adam da son alheri, da kuma kin kunci ko wahala, sannan ga tsoron talauci ko shiga
wahala a rayuwa.

 

Don haka ake ta fafutuka na neman falalar Allah ta dukiya don aji dadin gudanar da rayuwa. Wato kowa yana kan tasa hanyar nema na sana’a, ko kwadago, ko dai duk wata hanya ta juya dukiya ko jawota ta dama da haggu.

Allah yana zaban wassu cikin bayin sa ya arzutasu da rabon dukiya mai yawa ta wani sanadi cikin hanyoyin nema da muke kayi.

 

Wassu sun dace sun tara dukiya ta halal, wassu kuwa sun tabe dukiyar su ba tsarki wato ba halal a
ciki, wassu kuwa su hado naman rago dana alade a tukunya guda su dafa suna ci wato masu gauraya halal da haram.

Tsabta irin ta addinin mu ta munana dukiyar haram garamu, an sanya ta kazantace abin kyama, tana kai mai ita ga halaka da gamuwa da fushin Allah. Madallah da rayuwar magabata na kwarai masu gudun dukiyar haram ga kansu da iyalan su, saboda tsoron dukiyar haram har gujewa abin duniya sukeyi gaba daya don suyi rayuwa mai nagarta da tsabta ta neman yardar Allah da rahmar sa.

Duk wanda Allah ya bashi dukiya ta halal ya godewa Allah ta hanyar bayar da hakkin Allah a ciki, sannan ya yawaita sadaka ga marayu, mabukata da marasa gata. Kuma ana kyautatawa iyaye, iyali, dangi, makwabta, da duk wanda yazo neman taimako.

 

Shaidan yana cusawa wassu masu dukiya rowa, matsin hannu, qanqamo da kin tallafawa kowa. To mu sani hakika dukiya da duk arzikin duniya na Allah ne, shiya baiwa wanda yaso a cikin mu, don haka mubi shiryarwar addinin mu wajen yawan alheri, da kwadaitar da junan mu yawan sadaka da kyauta.

 

Lallai sadaka da kyauta basa kawowa mai dukiya komi cikin dukiyar sa sai karin albarka, da yawaita…!

 

Daga: Sheikh Aliyu Said Gamawa

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...