Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gwamna Abdulfatah Ya Bukaci Sabbin Shugabannin KH Da Su Magance Matsalolin Albashi

0 183

Gwamnan jihar Kwara, Dr. Abdulfatah Ahmed, ya  rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi 16 da ke jihar.

 

Gwamnan ya caje sabbin shugabannin kananan hukumomin da su yi kokarin samar da hanyar magance matsalar rashin biyan albashi a kananan hukumomi.

 

Karanta wannan: Ɗabi’ar Kwanciya Rigingine Ga Mai Ciki Na Janyo Haihuwar Jariri Babu Rai – Binciken Kwararru

 

Gwamnan ya kuma caje sabbin shugabannin kananan hukumomin da su hada kai da duk wasu masu ruwa da tsaki da ya kamata don samar da  hanyoyin kudaden shiga ga kananan hukumomin da suke jagoranta, wanda ta hakan zai taimaka masu wajen gudunar da aiyuka da kananan hukumomi.

 

Karanta wannan: ‘Yan Sanda A Jihar Kwara Na Sayar Da Mutanen Da Suka Daɗe A Komarsu A Tsare Ga Matsafa AKan Naira Dubu 80

Gwamnan ya nuna rashin jin dadin sa a kan jinkirta biyan kudaden albashin ma’aikatan kananan hukumomi, da malaman makaranta, da sauran ma’aikata da abun ya shafa.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...