Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gwamnan Sani Bello Ya Sauke Kwamishinonin Sa

0 167

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya sauke kwamishinonin sa bayan kammala zaman majalisar zartarwa na jiha da ya gudana a yau laraba a Minna babban birnin Jihar ta Neja wanda gwamnan ya jagoranta.

 

Bayanin hakan na kunshe ne wata takardan sanarwa dake dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan Malam Jibrin Baba Ndace, sanarwar ta kara da cewar gwamnan ya bar sabbin kwamishinoni uku da ya nada wadanda suka hada da: kwamishina a ma’aikatan raya al’adun gargajiya, kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa, da kwamishinan harkar kifaye.

 

Gwamnan ya umarci daraktoci da sakatarorin ma’aikatun gwamnati da su cigaba da gudanar da aiyuka har zuwa lokacin da zaiyi sabbin nadi, hakazalika gwamnan ya dakatar da zaman majalisar zartarwa na jiha har zuwa lokacin da za’a nada sabbin kwamishinoni.

 

Gwamnan yayi godiya ga tsoffin kwamishinonin bisa ga hadin kai da gudunmuwar da suka bashi wurin aiwatar da kyakkyawan manufofin sa na ciyar da jihar Neja da al’ummarta gaba, ya kuma yi masu fatan alkhairi.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...