Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gwamnati Ta Haramta Tallata Kwaroron Roba A Gidajen Talabijin Da Rana

0 753

 

Gwamnatin kasar Indiya, a yau Talata ta shelanta hana tallata kwaroron roba da gidajen talabijin ke yi da ranar Allah, lamarin da ya haifar da cece-kuce a fadin kasar musamman ma ‘yan kungiyoyin da ke rajin tabbatar da kiyaye lafiyar jima’i

 

Ma’aikatar yada labarai ta kasar ta Indiya ta ce, haramun ne wani gidan talabijin ya yi tallar kwaroron roba daga karfe 6:00 na safe har zuwa karfe 10:00 na dare saboda kokarin gwamnati na hana budewa yara kanana ido kan harkokin jima’i

 

 

Ma’aikatar yada labaran a sanarwar da ta fitar da safiyar yau ta ce, bayan hujjoji da ta ke da su na yadda wasu gidajen talabijin ke maimaita tallan kwaroron roba babu kakkautawa, ta dauki gabarar kawo tsari cikin harkar tallan, ta yadda tallan ba zai shafi tarbiyyar yara da matasa a kasar ba

 

Sai dai likitoci da masu rajin tabbatar da lafiya da ingancin jima’i sun kalubalanci manufar ta gwamnati, inda suke cewa wannan doka ta sabawa dalilin da ya sa ake tallata kwaroron roba ga jama’a wanda illarsa ke da tasiri na kai tsaye ga al’umma

 

 

Masu kuka da batun takaita lokutan tallan sun bayyana cewa, tallan kwaroron roba ana yinsa ne don a kaucewa samun juna biyun da ka iya bayuwa ga haifar ‘ya’ya gabanin Fatiha, wanda hakan a baya-bayan ne ke kara karuwa a tsakakkanin matasa

 

Wani likitan mata mai suna Dakta Gauri Kaushik ya bayyana cewa takaita lokacin tallan kwaroron roba zuwa dare sam ba daidai bane musamman ma a wannan yanayi da mu ke ciki da indiya da kaso 13 na juna biyun da ake samu a kowace shekara na matasa ne wadanda basu yi aure ba, sannan kuma ga akalla zubar da ciki miliyan 15 a shekara

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...